Ilimi
Birtaniya Ta Ba Da Tallafin Fam Miliyan 19 Don Kare Sauyin Yanayi A Najeriya
Gwamnatin Birtaniya ta sanar da bayar da tallafin fam miliyan 19 domin gina asibitoci da makarantun zamani masu jure sauyin yanayi a Najeriya.
Sanarwar ta fito ne a wajen kaddamar da hadin gwiwa tsakanin Gwamnatin Birtaniya, da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da kuma gwamnatocin jihohin Kano da Jigawa, inda aka kaddamar da makarantu da cibiyoyin lafiya guda 84 da aka gina ƙarƙashin shirin Climate Resilient Infrastructure for Basic Services (CRIBS).
CRIBS wani shiri ne na kirkire-kirkire da nuni da sabon salo da zai kare muhimman ayyukan lafiya da ilimi daga barazanar sauyin yanayi.
Najeriya tana matsayi na biyu a duniya wajen fuskantar barazanar sauyin yanayi ga yara, inda miliyoyi ke fuskantar ambaliya, fari, da tsananin zafi a kowace shekara.
Daraktar shirin a Najeriya, Cynthia Rowe, ta bayyana cewa an tsara tsarin CRIBS ne domin tantancewa da ƙarfafa cibiyoyi 84 , da suka hada da cibiyoyin lafiya a matakin farko guda 39 da makarantu 45 a Kano da Jigawa, ta hanyar amfani da matakan da suka dace na kariya daga sauyin yanayi.
Ta ce kaddamar da waɗannan cibiyoyin wata babbar nasara ce da ke nuna hanyoyin magance barazanar sauyin yanayi.
A cewarta, Gwamnatin Birtaniya tana alfahari da tallafawa Gwamnatin Najeriya ta wannan tallafin na Miliyan 19 ga shirin CRIBS.
Cynthia Rowe ta ƙara da cewa, an yi wannan aiki ne ta hanyar haɗin gwiwar kungiyoyi da kwararru da suka haɗa da: Gwamnatin Tarayyar Najeriya, Gwamnatin Birtaniya, UNICEF, Bankin Duniya, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Sextant Foundation, JigSaw, Fab Inc, Crown Agent da shirin UK Lafiya.
“CRIBS ya nuna yadda gine-ginen da suka dace da sauyin yanayi za su iya inganta samun ayyukan yau da kullum ga al’ummomin da ke da rauni. Muna fatan wannan hakan zai zama abin koyi da za a yada a fadin Najeriya.
Cynthia ta ƙara da cewa wannan kaddamarwar ta yi daidai da manufofin ƙasa da na jihohi a fannin sauyin yanayi, lafiya da ilimi, sannan tana nuna ƙudirin Gwamnatin Birtaniya na tallafawa Najeriya wajen rage barazanar sauyin yanayi da inganta ayyukan yau da kullum.
“Wannan ƙaddamarwa shaida ce ga abin da haɗin zai iya cimmawa,” in ji wakiliyar UNICEF a Najeriya Wafaa Saeed.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
