Labarai
Giwa LG: Matar Shugaban Karamar Hukuma Ta Kaddamar da Makon Shayar da Nono
Matar Shugaban Karamar Hukumar Giwa, Hajiya Hadiza Ahmad Sama’ila Yakawada, ta kaddamar da Makon Shayar da Nono na Duniya na bana, tare da kira ga iyaye mata da mazajensu da su ba wa jarirai nono kacokam na tsawon watanni shida na farko.
A yayin kaddamarwar, Hajiya Hadiza ta bayyana cewa shayar da jarirai nono na da muhimmanci matuƙa wajen tabbatar da lafiyar yara da kuma inganta cigaban su tun daga ƙuruciya.
Ta kuma bayyana cewa makon yana da nufin wayar da kan jama’a musamman a tsakanin iyalai game da amfani da shayar da nono, tare da ƙarfafa gwiwar ma’aikatan lafiya da su ci gaba da fafutukar wayar da kai a fadin karamar hukumar.

A nata jawabin, Sakatariyar Lafiya ta Karamar Hukumar Giwa, Hajiya Salamatu Balarabe, wadda ta sami wakilcin Hajiya Talatu Bello, jami’ar kula da magunguna masu muhimmanci ta karamar hukumar, ta yabawa kokarin shugaban karamar hukumar, Alhaji Ahmad Sama’ila Yakawada, wajen ɗaukar matakai don tabbatar da ingantaccen kula da lafiya ga al’ummar yankin.
Ta ce karamar hukumar za ta ci gaba da himma wajen kyautata lafiyar uwa da yara a fadin Giwa.
COV/Magaji Yakawada
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
