Labarai
Ɗaruruwan Tsaffin Jami’an Tsaron Isra’ila Sun Roki Trump Ya A Dakatar Da Yakin Gaza
Wata tawagar jami’an tsaron Isra’ila da suka yi ritaya su 600 ciki har da tsaffin shugabannin hukumomin leƙen asiri sun aika wa Shugaban Amurka, Donald Trump wasiƙa domin neman ya matsa wa Isra’ila da ta gaggauta kawo ƙarshen yaƙin da ake a Gaza.
Jami’an sun ce “tunaninmu ne cewa Hamas ta daina zama wata barazana ga Isra’ila”.
“Amincin da kake da shi a wajen Isra’ilawa zai ƙara ba ka damar sanya Firaiminista [Benjamin] Netanyahu da gwamnatinsa a kan hanya daidaitacciya: A kawo ƙarshen yaƙin, a dawo da mutanen da ke tsare a kuma daina gallaza wa Falasɗinawa,” kamar yadda suka rubuta.
Roƙon nasu na zuwa ne daidai lokacin da rahotanni ke cewa Netanyahu na ƙoƙarin faɗaɗa ayyukan soji a Gaza yayin da tattaunawar tsagaita wuta da Hamas ke fuskantar cikas.
Isra’ila ta ƙaddamar da mummuman yaƙi a Gaza sakamakon hare-haren Hamas a Kudancin Isra’ila ranar 7 ga Oktoban 2023 inda aka kashe kusan mutum 1,200 sannan aka yi garkuwa da mutum 251 a Gaza.
Fiye da mutum 60,000 aka kashe sakamakon yaƙin da Isra’ila ta ƙaddamar a Gaza tun lokacin, kamar yadda ma’aikatar lafiyar Hamas ta shaida.
- ‘Ƙawayen Isra’ila sun fara ƙaurace mata’: Ƙasashen duniya sun fara juya wa Netanyahu baya
- Yadda Birtaniya da ƙasashen duniya 28 suka caccaki Isra’ila kan yaƙin Gaza
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
