Labarai
Isra’ila ta taƙaita shigar da kayan agaji Gaza
Hukumomi a Isra’ila sun ce gwamnatin ƙasar ta yanke shawarar taƙaita shigar da kayan agaji zuwa zirin Gaza, sannan za ta ɗan dakata ta buɗe bakin iyakar zirin daga Rafas.
Isra’ila ta ce ta ɗauki wannan matakin ne saboda abin da ta kira jan ƙafa da a cewarta Hamas ke yi wajen mayar da sauran gawarwaki da ke hannunsu.
Zuwa yanzu dai gawarwaki huɗu kawai Hamas ta miƙa, sannan akwai rahotannin da ke cewa ƙungiyar za ta miƙa wasu gawarwakin guda huɗu, amma ta ce nemo gawarwakin na da wahalar gaske.
Shi ma Donald Trump ya yi ƙorafi, inda ya buƙaci Hamas ta mayar da gawarwakin “kamar yadda aka yi alƙawari,” in ji shi.
Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ce wasu gawarwakin sun ɓace, kuma zai yi wahala a gano su.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
