Labarai
Isra’ila na ci gaba da ragargaza Birnin Gaza ta sama da ƙasa
Dakarun sojan Isra’ila na ƙara nausawa cikin wani yanki mai cike da jama’a a birnin Gaza, yayin da suke ci gaba da kai farmaki ta ƙasa domin ƙwace iko da babban birnin mafi cunkoson jama’a.
Ana iya ganin yadda hayaƙi ya turnuke sararin samaniya yayin da sojojin ke harba makaman atilare da luguden bama-bamai.
Dubban mutane sun gudu, wasu kuma sun maƙale saboda haɗarin da ke tattare da guduwar. Sama da mutane sittin ne aka ce an kashe a jiya kadai.
Isra’ila ta ce tana gudanar da bincike kan rahotannin da ke cewa dakarunta sun kai hari kan asibitin yara na Gazan.
Ta ce tana son kubutar da mutanenta da Hamas ta rike da su, da kuma fatattakar mayaƙan Hamas 3,000 a wurin da ta bayyana a matsayin “tungar mayaƙan ta ƙarshe”.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
