Connect with us

Ilimi

Gwamnan Jihar Kaduna Ya Ɗauki Nauyin Karatun Ɗaliban Kuriga

Published

on

Gwamna Uba Sani, na jihar Kaduna ya yi alkawarin bai wa ɗaliban Kuriga 137 da aka kubutar daga hannun ’yan bindiga tallafin karatu.

Uba Sani ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga daliban da suka kubuta daga hannun ‘yan bindiga a gidan gwamnatin jihar a ranar Alhamis.

Gwamnan ya ce gidauniyarsa ta Uba Sani za ta gyara makarantun Kuriga domin bai wa yara a garin damar samun ingantaccen ilimi.

Sani, ya Kara da cewar bayan sako daliban, gwamnatin jihar ta dauki masana ilimin halayyar dan adam aiki wadanda suka shafe lokaci suna tattaunawa da daliban don tabbatar da lafiyarsu.

Sai dai ya bayyana cewar ɗaya daga cikin malaman da aka sace, mai suna Malam Abubakar ya rasa ransa sakamakon matsalar rashin lafiya.

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta dauki nauyin karatun ’ya’yan malamin da ya rasu, tare da bai wa iyalansa kyautar Naira miliyan 10.

Sani ya ce, “Jiya iyayen daliban suka zo nan, sun hadu da yaran, kowa ya yi murna. Ina so na yaba wa yaran. Sun yi hakuri da mu. Sun kuma fahimci halin da suka tsinci kansu a ciki.

“Lokacin da suka dawo, mun fahimci wasu na cikin matsanancin hali. Wannan shi ne dalilin da ya sa muka dauko masana ilimin halayyar dan adam, wadanda suka ba su shawarwari. Na yi farin ciki kamar yadda yaran suka yi farin ciki.

“Kwana biyu da kubutarsu, sun nuna ba sa son komawa gida, sun so zama da ni a nan na tsawon mako biyu. Amma na sanar da su cewar ba zai yiwu ba dole su koma gida. Iyayensu na muradin ganin su bayan shafe kimanin kwana 17 a hannun ‘yan bindiga.”

Gwamnan ya kara da cewa, “Na kuma bayar da umarnin yin gyare-gyare a garin da kuma makarantunsu, domin Kuriga na daya daga cikin yankuna mafi zaman lafiya a Kaduna.”

 

Aminu Dalhatu

 

Labarai

Labarai20 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai22 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara