Connect with us

Kasuwanci

Gwamnatin Jihar Kwara Ta Dakatar Da Yanka Nama A Mahauta Na Kwanaki 3

Published

on

Gwamnatin jihar Kwara ta binne duk wani naman dabbobin da ake zargi yana dauke da guba don gujewa sayarwa mutane a  kusa da Kwalejin Kolejin Koyon Larabci da Shari’ar Musulunci ta Jihar Kwara (CAILS) da ke Ilorin.

 

Hakan ya biyo bayan wasu matakan da aka dauka na hana mutane cin naman dabbobin  da ake zargin yana dauke da  guba a jihar.

 

A cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar ma’aikatar noma da raya karkara, Madam Funke Sokoya ta fitar, ta ce gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar sauran masu ruwa da tsaki sun amince da dakatar da ayyukan yanka dabbobi har na tsawon kwanaki uku domin a samu damar yin feshin magani a  Mahautar don dakile duk wata cuta da ke gurin.

 

Sanarwar ta ce binciken farko ya nuna cewa mummunan lamarin ya faru ne sakamakon kiwo da gurbatacciyar ciyawa da ke kewaye da yankin.

 

Sanarwar ta bayyana cewa, ma’aikatar za ta kara sanya ido a sauran Mayanku  daban-daban na jihar domin tabbatar da tsaftar muhalli.

 

A nasa jawabin, Daraktan Kula da Dabbobi, Dokta Olugbon Saliman, ya ce, za a rage yawan Mahauta da ba na gwamnati ba zuwa matakin da ma’aikatar za ta iya sarrafawa.

 

Ya ce duk wata Mayanka  da ba ta bi ka’idojin gwamnati ba game da  tsafta, za a rufe ta.

 

Ali Muhammad Rabi’u

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Ilimi2 days ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Gidaje A Jami’ar Tarayya Da Ke Babura

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta ci gaba da tallafawa harkokin koyo da koyarwa a Jami’ar Fasaha ta Gwamnatin...

Labarai2 days ago

An Samar Da Sabon Tsari Da Zai Inganta Harkar Noman Rogo A Najeriya

Shugaban kungiyar masu noman rogo ta Najeriya (NCGA), Mustapha Othman Bakano, ya kaddamar da wani tsari na samar da kasuwa...

Labarai4 days ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Tarakta 300 Ga Manoma Daga Amurka

A kokarinta na ci gaba da habbaka harkokin noma, Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙulla wata yarjejeniyar haɗin gwiwa da wasu...

Labarai4 days ago

An kama masu zanga-zanga 17 a jami’ar Texas

An sake kama ƙarin mutanen da ke da alaƙa da zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinawa inda a wannan karon...

Labarai4 days ago

An Samar Da Masauki Kusa Da Harami Ga Alhazan Jihar Jigawa

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa  ta samar da katafaren masauki  kusa da Masallacin Harami da ke birnin Makkah...

Labarai7 days ago

Kungiyar AFAN Ta Shirya Taron Bita Ga Manoman Jihar Jigawa

Hadaddiyar kungiyar manoma ta kasa reshen Jihar Jigawa da cibiyar binciken yanayin kasa dake Kaduna sun shirya wa manoma daga...

Fasaha7 days ago

An Bukaci Gwamnatin Sakkwato Ta Agaji Jami’ar Jihar

Kungiyar Malaman Jami’ar Jihar Sakkwato ASUU-SSU ta yi kira ga gwamnatin Jihar ta duba halin da kungiyar ke ciki da...

Kasuwanci1 week ago

Mun Aika Musu Takardun Gargadi Kafin Ginin Ya Rushe – KANUPDA

  Manajan Daraktan Hukumar Tsare-tsare da Ci gaban Birane ta Jihar Kano (KNUPDA), Architect Ibrahim Yakub Adamu ya yi gargadin...

Ilimi1 week ago

Zamu Zuba Jarin Dala Miliyan 600 a Nijeriya – Mr. Robert

Shugaba Kasa Bola Tinubu ya samu masu zuba jarin dala miliyan 600 daga kamfanin sufurin jiragen ruwa na kasar Denmark,...

Labarai1 week ago

Gini Ya Fado Kan Mutane 11 A Kano

Wani gini ya fado kan ma’aikata suna tsaka da aikin gini a unguwar Kuntau da ke Karamar Hukumar Gwale a...

Mafi Shahara