Kasuwanci
Kwari Masu Lalata Amfanin Gona Sun Mamaye Gonakin Tumatur A Kano
Shugaban kungiyar manoma ta jihar Kano, AFAN, Abdullahi Maibreadi, ya bukaci gwamnati a dukkan matakai da su taimaka wa manoma wajen dakile yaduwar kwarin nan da ke lalata tumatur a gonaki.
Shugaban ya yi wannan kiran ne a wata hira da gidan rediyon Najeriya a Kano.
A cewar sa, kwarin sun mamaye gonakin tumatir a kananan hukumomin Bagwai da Shanono da Kura da Garin Malam da Bebeji, Bunkure da Rano da Kibiya da kuma wasu sassan Tudun Wada Dawakin Kudu.
Maibreadi ya bayyana cewa, rahoton da AFAN ta samu daga sassan kananan hukumomin ya nuna cewa gonakin Tumatir da suka kai hekta dubu hudu da dari shidda da ashirin da daya da kudinsu ya kai Naira biliyan daya ne a halin yanzu suka kamu da cutar, yana mai jaddada cewa idan ba a yi wani abu don ceto lamarin ba, nan da mako daya zuwa biyu masu zuwa, manoma za su yi asarar kusan Naira miliyan dubu goma zuwa dubu ashirin a Kano.
“Abin takaici shine akasarin manoman sun gama kashe kudi a gonakinsu, kuma shuka ta yi kyau, an kusa girbi sai kuma ga cutar ta bulla.”
Maibreadi ya jaddada bukatar gwamnati ta taimaka wa manoma da ingantaccen iri mai jure wa yanayi, yana mai cewa, manoman Kubewa suma sun sami bullar irin wannan annoba a kakar noman da ta gabata.
“Mu manoma ba mu da ikon samun wadannan irin shuka, amma idan gwamnati ta hada hannu da kamfanonin kasa da kasa, za su iya saye su sayar da su, ko kuma ba da tallafi ga manoma domin gujewa irin wannan babbar asara da ke kara shafar tattalin arzikin kasar.”
Shugaban ya bukaci manoma da su daina amfani da maganin kwari mara inganci domin gujewa asara.
Khadija Aliyu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
