Labarai
An Samar Da Masauki Kusa Da Harami Ga Alhazan Jihar Jigawa
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta samar da katafaren masauki kusa da Masallacin Harami da ke birnin Makkah na kasar Saudiyya ga Alhazan jihar da za su sauke farali a bana.
Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan ga wakilin gidan rediyon Najeriya a Dutse babban birnin jihar.
Ya ce hukumar ta samar da masauki mai daraja da zai yi gogayya da na sauran kasashen duniya kusa da masallacin Harami, domin baiwa Alhazan jihar damar zuwa masallacin ba tare da wata wahala ba.
Ya kuma bayyana cewa, Gwamna Umar Namadi ya kudiri aniyar bai wa hukumar duk wani tallafin da ya dace domin samun damar kulawa da Alhazan jihar yadda ya kamata.
Dangane da ciyarwa yayi aikin Hajji kuwa, Ahmed Labbo ya bayyana cewa, hukumar ta kulla yarjejeniya da wani kamfani don samar da ingantaccen abinci ga Alhazan jihar yayin gudanar da aikin Hajjin.
Ya ce, hukumar na da kwarin gwiwar cewa kamfanin zai cimma yarjejeniyar da suka kulla.
Shugaban ya yi nuni da cewa, za su rika bada kulawa ta musamman ga mahajjatan da ke fama da lalurar rashin lafiya don ganin su ma an samar musu abincin da ya dace da su.
Yayin da ya yaba wa ma’aikatan hukumar kan kwazon su, ya kuma umarce su da su sake sadaukar da kansu don ganin an samu nasarar aikin Hajjin bana.
Labbo ya bayyana godiya ga gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Umar Namadi da kuma hukumar Alhazai ta kasa NAHCON bisa goyon bayan da suke bai wa hukumar jin dadin alhazai ta jihar jigawa.
Usman Muhammad Zaria
-
Labarai4 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai5 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai5 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai5 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai4 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai3 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai3 days agoShugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
