Labarai
An kama masu zanga-zanga 17 a jami’ar Texas
An sake kama ƙarin mutanen da ke da alaƙa da zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinawa inda a wannan karon aka yi kamen a jami’ar Texas da ke Dallas.
Wata sanarwa daga jami’ar ta ce ƴan sandan sun je makarantar bayan da masu zanga-zangar suka fara kafa sansani a babbar hanyar shiga makarantar.
An ba su gargaɗi a rubuce kan cewa su bar wajen kafin ƴan sanda su kutsa kai tare da tarwatsa wajen.
Ya zuwa ƙarfe 5:00 agogon ƙasar (22:00 GMT) na ranar Laraba ƴan sanda sun ce sun kama mutum 17 kan laifin ƙetare iyaka.
Daga bisani kuma kafar yaɗa labarai ta CBS ta yi rahoton cewa mutum 21 aka kama inda ta ruwaito lauyoyin waɗanda aka tsare.
BBC
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
