Fasaha
Kasuwar Panteka Ta Kaduna Ta Samu Lasisin Koyar Da Sana’o’i —NBTE
Hukumar kula da ilimin fasaha ta kasa NBTE ta ce yanzu an shigar da Tsarin Kwarewar Kwarewar Ma’aikata a Tsarin Ma’aikata na Kasa.
Sakataren zartarwa na hukumar Farfesa Idris M. Bugaje ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen bikin kaddamar da ginin da gyaran kasuwar Panteka da gwamna Uba Sani ya yi a Kaduna.
Farfesa Bugaje ya lura cewa, wanda suka kamala samun horo a kasuwar Panteka za a iya daukar su aiki a kowane mataki na Gwamnati tare da takaddun shaida na kamala samun horo kuma masu sha’awar za su iya samun ayyukan yi a kasashen waje.
A cewarsa, tun a shekarar 2021 Panteka ta sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna domin saukaka tsarin koyar da sana’o’i a kasuwa.
“A yanzu Panteka ta zama tambari, wanda ake mutuntawa a fadin kasar har ma a kasashen ECOWAS da dama. Daga karshe Panteka ta zama wata cibiya.”
Sakataren zartarwa ya yi kira ga mambobin kungiyar bunkasa kasuwar Panteka da su bi ka’idojin da aka amince da su na shagunan da kuma samun tallafi daga masu ruwa da tsaki na waje domin sabbin gine-ginen da za ayi.
A nasa jawabin, Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya ce yayin wani taron masu ruwa da tsaki bayan samun rahoton faruwar gobara a kasuwar, ya yi alkawarin gyara kasuwar Panteka domin mayar da ita babbar cibiyar kasuwanci da fasaha a Arewacin Najeriya.
Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa taron ya yi ne domin cika alkawarin da ya dauka na gyara Kasuwar da kayan aiki na zamani da hanyoyin da za a bi domin jawo hankalin masu goyon baya daga wasu jihohi da kuma bunkasa harkokin kasuwanci a Kasuwar.
“Wannan aikin zai samar da dubunnan ayyukan yi kai tsaye a jiharmu, zai kara mana kudaden shiga da ake samu a cikin gida, zai rage zaman kashe wando a tsakanin matasa da kuma jawo hankulan masu zuba jari zuwa jihar Kaduna, inda matasa ke koyon sana’o’in hannu da samun aikin yi.
Ya kara da cewa, kasuwar idan aka kammala za ta kasance wata babbar cibiya ta sana’o’i da fasahar kere-kere a Arewacin Najeriya, ya bukaci ‘yan kwangilar da su jajirce wajen ganin an gaggauta kammala aikin da ke da dimbin fa’ida ga jama’a da jihar Kaduna.
Tun da farko Shugaban Kasuwar Panteka, Alhaji Sule Shehu ya nuna godiya ga Gwamna Uba Sani bisa cika alkawuran da ya dauka na gyara kasuwar.
COV/AMINU DALHATU/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
