Ilimi
Hukumar Kwastam Na Binciki Kisan Da Aka Yi A Kano
Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kaddamar da bincike kan zargin kisan da aka yi wa Abdullahi Abdulwahab Magaji, ma’aikaci a hedikwatar Hukumar a Abuja, wanda ke zaune a unguwar Farm Center dake, Kano.
Shugaban Kwastam na Kano/Jigawa Dauda Chana ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano.
Ya ce lamarin ya faru ne a gidan marigayin da ke karamar hukumar Tarauni.
Chana ya bayyana cewa an baiwa hukumar kwastam da ‘yan sanda izinin gudanar da bincike mai zurfi domin kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika, kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya na gudanar da bincike kan lamarin.
Hukumomi na yin kira ga mazauna yankin musamman makwaftan marigayin da su fito da sahihan bayanai domin a samu nasarar cafke wadanda ke da hannu a kisan.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
