Labarai
Hukumar Kwastam Ta Kwace Kayayyaki na Sama da Naira Miliyan 82 A Bauchi
Daga Alhassan Usman
Sashen Ayyuka na Tarayya, da ke Yanki na 4 a Bauchi, na Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) wato Zone D, ya kwace kayayyakin fasa-kwauri da darajar harajinsu ta kai sama da Naira Miliyan 82 cikin makonni biyu.
Kwamandan Yankin, Abdullahi Kaila, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Bauchi, inda ya ce jami’an sashen yaki da fasa-kwauri sun yi nasarar kwace kayayyakin tsakanin ranakun 8 zuwa 19 ga watan Disamban 2025.
Ya bayyana cewa Sashen na Ayyukan Tarayya ne ke da alhakin aiwatar da dokokin Kwastam, bin manufofin haraji na gwamnati da kuma dakile fasa-kwauri a jihohi tara, wadanda suka hada da Adamawa, Taraba, Bauchi, Gombe, Borno, Yobe, Plateau, Benue da Nasarawa.
Kaila ya kara da cewa an kara karfafa ayyukan yaki da fasa-kwauri a yankin, ta hanyar inganta hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu sa ido, yana mai jaddada cewa irin wannan hadin gwiwar na kara musayar bayanan sirri da aiwatar da ayyukan hadin kai wajen yakar kungiyoyin fasa-kwauri.
Ya bukaci ‘yan kasuwa a yankin da su kasance masu bin doka, su kuma guji haramtaccen kasuwanci, yana mai gargadin cewa ba za a bar wata mafaka ga masu aikata fasa-kwauri ba.
Kwamandan ya kuma ce sashen zai ba da muhimmanci ga wayar da kan jama’a, ta hanyar amfani da kafafen yada labarai da kuma kai ziyara yankuna daban daban, domin fadakar da jama’a game da illar fasa-kwauri ga tattalin arziki da kuma karfafa su su rika kai rahoton haramtattun ayyuka.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
