Ilimi
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Kiwon Lafiya ta Tarayya Azare Zuwa Sunan Sheikh Dahiru Bauchi
Daga Bello Wakili
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sanar da sauya sunan Jami’ar Kiwon Lafiya ta Tarayya dake Azare a Jihar Bauchi, domin girmama marigayi shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai Jihar Bauchi, inda ya yaba da irin gudunmawar da marigayi malamin ya bayar tsawon rayuwarsa wajen bauta wa Allah, hidimtawa al’umma da ma ƙasa baki daya.

Ya bayyana Sheikh Dahiru Usman Bauchi a matsayin babban malami mai daraja, wanda ya zamto abin koyi ga al’ummar Najeriya, wanda kuma koyakoyarwabisa gaskiya, riƙon amana da kyawawan halaye suka yi tasiri mai kyau ga al’ummomi da dama a faɗin ƙasar.

-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
