Ilimi
Gwamnatin Zamfara Za Ta Gina Dakunan Kwanan Dalibai a Jami’ar Talata Mafara
Daga Aminu Dalhatu
Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanar da shirin gina dakunan kwanan dalibai da kuma samar da motocin sufuri ga Jami’ar Jiha da ke Talata Mafara, a wani bangare na kokarin inganta saukin shiga makarantar ga dalibai.
Gwamnan jihar, Dakta Dauda Lawal, ya bayyana hakan yayin jawabin da ya gabatar a bikin karbar sabbin dalibai karo na biyar da aka gudanar a harabar jami’ar da ke Talata Mafara, a karamar hukumar Talata Mafara ta jihar.

Gwamnan, wanda mataimakinsa Mani Malam Mummuni ya wakilta, ya jaddada cewa gwamnatinsa ta ayyana dokar ta-baci a bangaren ilimi, kuma tana da kudurin samar da kayayyakin fasaha na zamani domin tabbatar da ingantaccen ilimi a jami’ar.
Gwamna Lawal ya kuma bayyana godiyarsa ga abokan hulda na jami’ar, ciki har da TETFUND, shirin tallafin Gwamnatin Tarayya, da sauransu, bisa hadin gwiwar da suke bayarwa wajen tafiyar da jami’ar cikin nasara.
Ya taya sabbin daliban murnar samun gurbin karatu, tare da gargadinsu da su guji magudin jarabawa, shiga kungiyar asiri, shan miyagun kwayoyi, da sauran dabi’un da za su iya kawo cikas ga karatunsu.
Tun da farko, Shugaban Jami’ar Farfesa Abdullahi Ibrahim Tsafe, ya bayyana cewa dalibai 980 aka karba a zangon karatu na shekarar 2025/2026.

Farfesa Tsafe ya kuma nuna godiya ga gwamnatin jihar bisa dora masa nauyin jagorancin jami’ar, tare da tabbatar da cewa zai yi iya kokarinsa wajen cika amanar da aka dora masa.
Ya kuma bayyana wasu nasarorin da jami’ar ta samu, tare da kalubalen da ke bukatar a magance su.
Sarkin Mafara, Alhaji Bello Muhammad Barmo, shi ma ya yi jawabi a wajen taron, inda ya jaddada muhimmancin neman ilimi ga kowa, tare da yin nuni da ayoyi da hadisai na Manzon Allah (SAW) da ke nuna darajar ilimi.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
