Ilimi
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alkawarin Inganta Hanyoyi, Ruwa da Wutar Lantarki a Jami’ar FUD
Daga Usman Muhammad Zaria
Minista a Ma’aikatar Ayyuka, Barrista Bello Muhammad Goronyo, ya yi alkawarin shiga tsakani wajen samar da ruwa, hanyoyi da kuma wutar lantarki mai amfani da hasken rana ga Jami’ar Tarayya ta Dutse (FUD) da ke Jihar Jigawa.
Ministan ya bayyana hakan ne lokacin da Shugaban Jami’ar, Farfesa Ahmad Muhammad Gumel, tare da tawagarsa suka kai masa ziyarar ban girma a Abuja.
Barrista Goronyo ya taya shugaban jami’ar murnar nadin da aka yi masa, inda ya ce FUD jami’a ce mai tasowa wadda ke bukatar goyon bayan masu ruwa da tsaki domin ta cimma nasara. Ya kara da cewa ilimi yana daga cikin manyan manufofin “Sabunta kudurori” na Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, domin ilimi shi ne ginshikin cigaban al’umma.

Ya ce zai mika bukatar shugaban jami’ar dangane da hanyoyi ga Babban Ministan Ayyuka, Injiniya David Umahi, sannan a matsayinsa na mai kula da Hukumar Kula da Gyaran Hanyoyi ta Tarayya (FERMA), zai yi kokarinsa wajen taimakawa wannan sabuwar jami’a. Ya kuma kara da cewa zai tuntubi Ministan Albarkatun Ruwa domin taimaka wa jami’ar da ayyukan ruwa don saukaka rayuwar dalibai.
Haka kuma, Barrista Goronyo ya shaida wa shugaban jami’ar cewa zai dauki batun samar da lantarki mai amfani da hasken rana tare da Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara (REA), inda gwamnati ke kokarin magance matsalar wutar lantarki ta hanyar wasu shirye-shiryen gwaji a manyan makarantun gaba da sakandare.
Ministan ya karfafa wa shugaban jami’ar gwiwa da ya rika ziyartar sauran ma’aikatu da hukumomi domin neman hadin gwiwa da goyon baya don bunkasa wannan sabuwar jami’a.

Tun da farko, a nasa jawabin, Farfesa Gumel ya gode wa Ministan bisa karbar su, yana mai cewa FUD jami’a ce mai tasowa wadda ke bukatar tallafi musamman a fannoni kamar hanyoyi, dakunan kwanan dalibai, ruwa da wutar lantarki.
Ya ce duk da karancin shekarun jami’ar, tana daga cikin mafi nagarta a cikin jami’o’in da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya kafa, har ma tana zarce wasu tsofaffin jami’o’i a wasu fannoni.
Ya yaba da irin nasarorin da Ministan ya samu tun bayan hawansa kan mulki, tare da addu’ar Allah Ya ba shi nasara a dukkan ayyukansa.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
