Kasuwanci
Matan da Mazajensu Suka Rasu Sun Sami Tallafin Kayayyakin Sana’o’i a Jihar Kwara
Daga Ali Muhammad Rabi’u
Aƙalla matan da mazajensu suka rasu su 600, da matasa ne suka sami tallafin kayan aiki, da na abinci da kyautar kuɗi daga mamba da ke wakiltar Gundumar Ilori ta Kudu a Jihar Kwara, domin su zama masu dogaro da kansu.
A yayin taron ƙarfafawar mai taken “Daga Mafarki zuwa Gaskiya: Shekaru Biyu na Cimma Nasara a Gundumar” (Iwosan Tesiwaju 4.0) mamba da ke wakiltar Gundumar Ilorin Kudu a Majalisar Dokoki ta Jihar Kwara Maryam Yusuf Aladi ta shirya, Shugaban APC na Jihar Kwara, Prince Sunday Fagbemi, ya ce manufar wannan shirin shi ne fitar da mutane daga kangin talauci.
Shugaban jam’iyyar wanda mai ba gwamnan Jihar Kwara shawara kan harkokin siyasa, Sulyman Abubakar, ya wakilta, ya gode wa mambobin jam’iyya bisa goyon bayan da suka nuna ga shugabancin hangen nesa a jihar.

A cewarsa, dukkan mambobin jam’iyya da sauran mazauna jihar za su amfana da mulkin dimokuradiyya kamar yadda jam’iyyar ta yi alkawari.
Prince Fagbemi ya bayyana cewa ƙarfafawa ga matan da mazajensu suka rasu da sauran mutane wani kyakkyawan mataki ne na rage wahalhalun da suke fuskanta.
Ya gode wa Maryam Yusuf Aladi bisa hangen nesanta wajen taimakawa marasa galihu a cikin al’umma.

A jawabinsa, Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Kwara, Yakubu Danladi-Salihu, wanda Seun Ogunniyi ya wakilta, ya ce a koyaushe Majalisar tana ƙarfafasu wajen ganin suna tallafawa al’umma domin inganta rayuwar talakawa.
Ya yi kira ga sauran mambobi su bi sahun waɗanda suka tallafa wa marasa galihu domin rage rashin aikin yi a cikin al’umma.
A sakonta na alheri, shugabar mata ta APC a Jihar Kwara, Hajiya Falilat Mohammed, ta yabawa ‘yar Majalisar bisa tallawa waɗanda ke cikin buƙata.

Ta ce da yawa daga cikin waɗanda suka amfana suna buƙatar ƙaramin abu ne kawai don su fara wata sana’a.
Hajiya Falilat ta bukaci waɗanda suka amfana su tabbatar sun yi amfani da kayayyakin da kuɗin da aka ba su yadda ya dace.
A jawabinta, shugabar mata ta APC a majalisar dattawa, Hajiya Tawakalitu Agaka, ta nuna farin ciki da wannan shiri na tallafa wa marayu da marasa galihu.
Ta shawarci waɗanda suka amfana da kada su sayar da kayan da aka ba su.

A nasa bangaren, Shugaban Karamar Hukumar Ilorin Kudu na Jihar Kwara, Nuhu Podo, ya y> kira ga dukkan mambobin jam’iyya su tabbatar sun samu muhimman takardu kamar lambar shaidar kasa da katin zabe domin su sami karin fa’idodin gwamnati daga matakin jihar da tarayya.
Tunda farko a jawabinta, Maryam Yusuf Aladi, memba mai wakiltar Gundumar Ilorin Kudu a Majalisar Dokoki ta Jihar Kwara, ta ce an yi wannan ƙarfafawa ne don tallafa wa mutanen da ke cikin gundumar.
Ta bukaci waɗanda suka amfana su ɗauki wannan tallafi a matsayin damar fara kasuwanci wanda zai ba su damar tallafa wa iyali.
Kayayyakin da aka raba sun haɗa da: da Injin Wanki, Injin Busar da kai, Fanka mai amfani da hasken Rana, Injin Niƙa, Keken Dinki da Firiji da sauransu.
-
Ilimi7 days agoFarfesa Gumel Ya Fitar da Sabon Tsari da Zai Daga Martabar FUD
-
Labarai3 days agoHukumar Raya Kogin Benuwe Ta Bullo da Sabuwar Fasahar Kare Hanyar Ban-ruwa a Tafkin Geriyo
-
Ilimi3 days agoAn Gudanar da Liyafar Taya Murna ga Sabon Shugaban Jami’ar Tarayya Dutse
-
Labarai5 days agoGwamnatin Tarayya ta Bada Tallafin Kayayyakin Aiki Gona ga Ƙananan Manoma a Jigawa
-
Labarai6 days agoAn Fara Bikin Kamun Kifi da Al’adu na Ƙasa da Ƙasa na Argungu na Bana
-
Labarai4 days agoGwamnatin Jigawa ta Amince da Shirin Ciyarwar Watan Ramadan na Bana
-
Labarai6 days agoHukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta Ja Hankalin Maniyyata Game da Muhimmancin Halartar Taron Bita
-
Labarai6 days agoJigawa: Hukumar Alhazai ta Bai wa Amirul Hajji Tabbacin Cikakken Goyon Baya
