Labarai
Gwamnatin Jigawa ta Baiwa Kungiyar Tsoffin Sojoji Gagarumar Gudummawa
Daga Usman Muhammad Zaria
Kungiyar Tsoffin Sojoji reshen jihar Jigawa ta samu tallafin sama da naira miliyan 40 a wajen taron kaddamar da Gidauniyar Tallafawa Kungiyar na bana, wanda aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana matuƙar godiyarsa ga irin sadaukarwar da mambobin Legion suka yi, ciki har da waɗanda suka sadaukar da rayukansu wajen hidimtawa ƙasa.

Ya jaddada cewa irin wannan sadaukarwa za ta ci gaba da kasancewa a tarihin ƙasa, tare da tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Jigawa da al’ummar jihar za su ci gaba da nuna godiya da tallafa wa tsoffin sojojin domin samun ingantacciyar rayuwa.
Gwamna Namadi ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 10 daga gwamnatin jihar, tare da tasa gudummawar ta Naira miliyan 2. Mataimakin Gwamna, Injiniya Aminu Usman, shi ma ya bayar da Naira miliyan 2, yayin da ƙananan hukumomi 27 na jihar suka bayar da gudummawar haɗin gwiwa ta Naira miliyan 13.

Sauran manyan gudummawa sun haɗa da na mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar, Shugaban Ma’aikatan Gwamnati (Head of Service), Manyan Mataimaka da Masu Ba Gwamna Shawara na Musamman, shugabannin hukumomin tsaro, da kuma Kungiyar ‘Yan Jaridu ta Correspondents’ Chapel, wadda ta bayar da Naira dubu 100.
A jawabin, Shugaban Kungiyar Tsoffin Sojojin Nijeriya a Jihar Jigawa, Malam Aliyu Mustapha, ya gode wa gwamnatin jihar da al’ummar jihar baki ɗaya bisa ƙauna, tausayi da girmamawa da suke nuna wa mambobin Legion.

Ya bayyana cewa irin wannan kyakkyawar mu’amala tana ƙara ƙarfafa gwiwar kowa a cikin al’umma, tare da nuna cewa ba a manta da sadaukarwar da suka yi a baya ba.
“Ga ’yan uwana tsoffin sojoji, ina tabbatar muku da cewa Gwamnatin Jihar Jigawa na tsaye daram tare da mu,” in ji Shugaban.
“Ina matuƙar jin daɗin wannan karamci, kuma ina sake tabbatar da kudurin Kungiyar Tsoffin Sojojin Najeriya na ci gaba da fafutuka da hulɗa tare domin inganta walwalar dukkan mambobin Legion a faɗin jihar.”
-
Ilimi7 days agoFarfesa Gumel Ya Fitar da Sabon Tsari da Zai Daga Martabar FUD
-
Labarai3 days agoHukumar Raya Kogin Benuwe Ta Bullo da Sabuwar Fasahar Kare Hanyar Ban-ruwa a Tafkin Geriyo
-
Ilimi3 days agoAn Gudanar da Liyafar Taya Murna ga Sabon Shugaban Jami’ar Tarayya Dutse
-
Labarai5 days agoGwamnatin Tarayya ta Bada Tallafin Kayayyakin Aiki Gona ga Ƙananan Manoma a Jigawa
-
Labarai6 days agoAn Fara Bikin Kamun Kifi da Al’adu na Ƙasa da Ƙasa na Argungu na Bana
-
Labarai4 days agoGwamnatin Jigawa ta Amince da Shirin Ciyarwar Watan Ramadan na Bana
-
Labarai6 days agoHukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta Ja Hankalin Maniyyata Game da Muhimmancin Halartar Taron Bita
-
Labarai6 days agoJigawa: Hukumar Alhazai ta Bai wa Amirul Hajji Tabbacin Cikakken Goyon Baya
