Connect with us

Labarai

Hukumar Kwastam ta Kaddamar da Ayyukan Tallafin Al’umma a Maigatari

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria 

Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam na kasa  Bashir Adewale Adeniyi ya sake jaddada kudirin hukumar na inganta rayuwar al’umma baya ga tara kudaden shiga da kula da kan iyakoki ba, inda ya kaddamar da gyaran dakunan karatu, bandakuna da kuma rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana a Makarantar Firamare ta Malam Alhassan da ke Karamar Hukumar Maigatari a Jihar Jigawa.

Adeniyi ya ce aikin na nuni da aniyar hukumar na karfafa dangantaka da al’umma tare da bayar da gudunmawa mai ma’ana ga ci gaban kasa, musamman a yankunan iyaka masu zaman lafiya kamar Maigatari.

Ya kuma bukaci mazauna yankin da wadanda za su amfana da su kula da kayayyakin yadda ya kamata domin samar wa yara makoma mai kyau.

Babban Kwanturolan ya bayyana cewa wannan tallafi na daga cikin shirye-shiryen Ayyukan Tallafin Al’umma (CSR) na hukumar, wanda ya hada da gyaran cibiyar lafiya a yankin.

A jawabinta, Mai kula da shiyyar NP ta Hukumar Kwastam, Misis Umoh, ta ce a karkashin jagorancin Adeniyi, shirin CSR ya zama daya daga cikin manyan ginshikan hukumar. Ta ce an kaddamar da sashen CSR a watan Maris na shekarar 2025 a Wuse, Abuja, domin dacewa da manufar sabunta kudurori na Sgugaba Tinubu wato Renewed Hope.

Ta kara da cewa ayyukan CSR sun hada da bayar da tallafin karatu, ginawa da gyaran azuzuwa, hako rijiyoyi, rabon kayan abinci da sauran ayyukan ci gaban al’umma.

A cewarta, tun bayan fara shirin, an gudanar da ayyuka da dama a yankunan da hukumar ke aiki a fadin kasar nan.

A matsayin wani bangare na tallafin da aka bayar a Makarantar Firamare ta Malam Alhassan, an raba kayan karatu sama da guda 1,800 ga dalibai domin inganta koyo da koyarwa.

Ita na a nata jawabin Kwanturola da ke kula da sashen CSR, Kwanturola NP Ibrahim, ta ce shirin “Customs Care” na nuna hangen nesan hukumar na fadada aikinta daga tara kudade kawai zuwa samar da tasiri mai kyau ga al’umma.

Ta kara da cewa kayayyakin da aka samar za su taimaka wajen rage gibin da ake fuskanta a bangaren ilimi, tare da tabbatar da cewa sashen CSR zai ci gaba da fadada ayyukansa domin amfanar  al’umma.

A sakonnin godiya nasu, Shugaban Karamar Hukumar Maigatari, Usman Na’Allah, da wani jagoran al’umma, Alhaji Isa Dangalan, sun yaba wa Hukumar Kwastam ta kasa bisa wannan tallafi.

Gwamnan Jihar Jigawa Umar Namadi, wanda Kwamishinan Kasafi, Alhaji Babangida Umar Gantsa ya wakilta, ya  nuna godiyarsabisa wannan karamci, inda ya bayyana tallafin a matsayin abin da zai kara taimaka wa kokarin gwamnati na inganta kayayyakin more rayuwa a bangaren ilimi a jihar.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara