Labarai
Gwamnatin Kano Ta yi Karin Girma ga Ma’aikata 130
Daga Khadijah Aliyu
Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano ta amince da karin girma ga ma’aikata 130 a fannoni daban-daban na aikin gwamnati a jihar.
An amince da karin girman ne a yayin taron Hukumar na wata-wata, inda mambobi suka duba tare da tantance ma’aikatan da suka cancanci karin matsayi, da nazarin wasu batutuwan gudanarwa da suka hada da bukatun canjin aiki da kuma shari’o’in ladabtarwa.
Shugabar Hukumar, Hajiya Ladidi Ibrahim Garko, ta ce karin girman na daga cikin nauyin da kundin tsarin mulki ya dora wa hukumar, na tabbatar da bin ka’idoji da dokokin aikin gwamnati.
Ta kuma bukaci ma’aikatan gwamnati da su ci gaba da jajircewa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, tana mai jaddada cewa gwamnatin jihar na goyon bayan ma’aikata masu ƙwazo da jajircewa, amma ba za ta lamunci sakaci ko rashin da’a a wurin aiki ba.
A nasa jawabin, Kwamishina a Hukumar Kula da Ayyukan Ma’aikatan Gwamnati ta Kano, Alhaji Abdullahi Mahmud Umar, ya jaddada muhimmancin sadaukarwa da ƙwarewa a aiki, yana mai cewa hukumar na ci gaba da kyautata wa ma’aikatan da suka cancanta tare da tabbatar da inganci a aikin gwamnati.
Shi ma a nasa bangaren, babban sakataren hukumar, Alhaji Sani Shehu Minjibir, ya nuna gamsuwa da yadda taron ya gudana, yana mai tabbatar da cewa an yanke dukkan hukuncin ne bisa ga dokoki da ƙa’idojin aikin gwamnati da aka tanada.
Karin girman na daga cikin ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi na ƙarfafa gwiwar ma’aikata da kuma inganta ayyukan a ma’aikatu, da hukumomin gwamnati.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
