Labarai
Sabon Sufeto Janar Ya Sha Alwashin Kawar da Cin Hanci da Rashawa a Tsakanin ‘Yan Sanda
Daga Bello Wakili
Sabon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Tunji Disu, ya bayyana godiyarsa ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce naɗin nasa ya zo masa a matsayin ba-zata.
Da yake magana jim kaɗan bayan bikin kaddamar da shi a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, sabon shugaban ‘yan sandan ya gode wa Shugaban Ƙasa bisa amincewar da aka nuna masa.
Dangane da abubuwan da zai fara mayar da hankali a kai, Sufeto Janar ɗin ya ce zai fara da sake wayar da kan jami’ai da ma’aikata domin su fahimci cewa jama’a su ne ginshiƙin aikin ‘yan sanda.
Ya jaddada cewa babu wata rundunar ‘yan sanda a ko’ina cikin duniya da za ta yi nasara ba tare da haɗin kan jama’a ba, inda ya ƙara da cewa inganta walwalar jami’ai zai zama muhimmin mataki wajen ƙara ƙwazo da ƙwarewa a aiki.
Sufeto Janar ɗin ya sha alwashin kare haƙƙin ɗan Adam tare da ɗaukar matakin rashin haƙuri kan cin hanci da rashawa a tsakanin jami’an ‘yan sanda.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
