Labarai
‘Yan Sanda Sun Kama Wani Da Ake Zargi Da Kisan Abokinsa A Kano
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani mutum mai suna Sadiq Zubairu, bisa zargin kisan abokinsa Bello Bukar Adam wanda ma’aikacin kamfanin rarraba wutar lantarki take wato KEDCO.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ya ce a ranar 5 ga watan Mayu ne rundunar ‘yan sanda ta samu ƙorafin ɓatan Bello Bukar Adam mai shekara 45, wanda aka ce ya bar gida tun ranar 4 ga watan Mayun.
Sanarwar ta ce a ranar ne kuma ‘yan sanda suka samu rahoton tsintar gawar mutumin, wanda aka jefar a ƙauyen Bechi da ke yankin ƙaramar hukumar Kumbotso, inda nan take rundunar ‘yan sanda ta tura tawaga ta musamman ƙarƙashin jagorancin DPO na ƙaramar hukumar, inda suka ɗauko gawar zuwa asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, likitoci kuma suka tabbatar da mutuwarsa.
Daga nan rundunar ‘yan sanda ta ƙaddamar da bincike tare da kama wani mutum mai suna Sadiq Zubairu mai shekara 35 da ke unguwar Hotoron Arewa bisa zargin aikata laifin.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce a lokacin da ‘yan sandan ke tuhumar wanda ake zargin, ya amsa cewa ya haɗa baki da wasu mutum biyu wajen fito da Bello, wanda ya kasance abokinsa ne daga gidansa.
Sadiq ya shaida wa ‘yan sanda cewa da kansa ya ɗaure Bello inda suka rika dukansa da sanduna da ƙarafa masu kaifi a kansa da sauran sassan jikinsa har sai da ya mutu.
“Bayan ya mutu ne suka sanya shi jikin but ɗin motarsa, tare da jefar da gawar a kan titin Eastern Bypass, a daidai ƙauyen Bechi, inda suka gudu da motar, ƙirar Toyota Corolla 2015, da kuma wayar marigayin’‘, kamar yadda sanarwar ‘yan sandan ta yi bayani
Haka kuma wanda ake zargin ya shaida wa ‘yan sandan cewa dalilinsu na aikata hakan shi ne marigayin ya karɓi kuɗi har naira miliyan uku daga wajensa da nufin zai sama masa aiki, amma sai daga baya ya fahimci cewa marigayin ba zai sama masa aikin ba, kan hakan ne ya haɗa baki da wasu mutum biyu domin kashe shi tare da yin awon gaba da motarsa, inda suka ɓoyeta a wani gareji da ke unguwar Hotoro.
Tuni dai ‘yan sanda suka kwato motar.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
