Labarai
‘Yan Sanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 33 A Nasarawa
Rundunar ‘yan sanda ta kama wasu ƙasurguman masu garkuwa da mutane 33 da suka addabi sassa daban-daban a Jihar Nasarawa.
Cikin wadanda aka kama har da waɗanda suka yi garkuwa da wasu ɗaliban Jami’ar Tarayya ta Lafiya da ke Unguwar Gandu a yankin Mararaba na jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Shehu Umar Nadada a yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a hedikwatar rundunar a ranar Alhamis a Lafiya ya bayyana cewa, an kama dukkan waɗanda ake zargin ne a maɓoyarsu daban-daban.
“Waɗanda aka kama su 13 ne da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, 11 kuma ana zargin ’yan fashi da makami ne, sai ɗaya da ake zargin ɓarawon shanu ne da kuma waɗanda ake zargi da aikata fyaɗe su biyar, ciki har da wasu mutane biyu da ake zargin su da zamba”. Inji kwamishinan.
Ya kara da cewa, wadansu mutane da ‘yan sanda suka kubutar da su ne daga hannun masu garkuwa da mutane a watan Afrilun da ya gabata sun gano ɗaya daga cikin waɗanda suka yi garkuwa da su mai suna Shagari Ibrahim na garin Kadarko da ke Ƙaramar Hukumar Keana, inda nan take aka kama shi.
Shagari Ibrahim ya amsa laifinsa tare da tabbatar da cewa su ne suka sace wasu daliban Jami’ar Tarayya da ke Lafiya.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
