Labarai
Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Zamfara Ya Gudanar da taron Jin Ra’ayoyin Jama’a a Anka da Bukkuyum
Daga Aminu Dalhatu
Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Zamfara, CP Ahmad Muhammad Bello, ya gudanar da tarukan tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki da kuma jama’a a ƙananan hukumomin Anka da Bukkuyum, a wani ɓangare na ƙoƙarin da ake yi na ƙarfafa tsarin ‘Yan Sandan Al’umma wato “community policing” da kuma inganta tsaro a faɗin jihar.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan Sanda, DSP Yazid Abubakar, ya fitar, an bayyana cewa tarukan sun samar da damar tattaunawa kai-tsaye tsakanin ’yan sanda da al’ummomin yankunan.

Sanarwar ta ce a yayin zaman, Kwamishinan ya wayar da kan mahalarta kan muhimman batutuwan tsaro, inda ya jaddada muhimmancin faɗakarwa, gaggauta bayar da bayanan sirri, da kuma haɗin kai wajen yaki da laifuka da masu aikata su.
CP Bello ya bayyana cewa ingantaccen aikin ’yan sanda ba zai yiwu ba sai da cikakken goyon baya da haɗin kan jama’a

Ya kuma shawarci mazauna yankunan da su kasance masu bin doka, su rika kai rahoton duk wani abin zargi cikin gaggawa, tare da guje wa ɓoye ko kare masu aikata laifi a cikin al’umma.
A yayin ziyarar tasa, Kwamishinan ya kai ziyarar girmamawa ga Sarkin Zamfaran Anka kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad, CON, da kuma Sarkin Danko Bukkuyum, Alhaji Muhammad Usman, inda ya nemi ci gaba da goyon bayansu wajen inganta zaman lafiya, haɗin kai da tsaro a yankunansu.

Masarautun sun yaba da matakan da rundunar ’yan sanda ke ɗauka na tunkarar matsalolin tsaro, tare da yin alƙawarin ci gaba da haɗin gwiwa da hukumomin tsaro wajen magance matsalolin tsaro a jihar.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
