Connect with us

Labarai

Rukunin Farko na Maniyyatan Jihar Jigawa Ya Tashi Zuwa Kasar Saudiyya

Published

on

Rukunin farko na maniyyata 480 daga Jihar Jigawa ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Nuhu Muhammadu Sunusi da ke Dutse zuwa birnin Madina na kasar Saudiyya domin aikin Hajjin 2026.

Babban Daraktan Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya jim kaɗan bayan tashin jirgin nasu zuwa ƙasar mai tsarki.

Ya bayyana cewa maniyyatan sun fito ne daga ƙananan hukumomi 25 na jihar.

Ya ce ƙananan hukumomin sun haɗa da Kazaure, Roni, Gwiwa, Yankwashi, Gumel, Gagarawa, Garki, Maigatari, Suletankarkar, Babura, Jahun, da Miga.

Sauran sun haɗa da Kafin Hausa, Auyo, Hadejia, Kirikasamma, Guri, Birniwa, Malam Madori, Dutse, Kiyawa, Ringim da Gwaram.

Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana cewa jirgin ya kuma ƙunshi wasu jami’an hukumar jin daɗin alhazai ta jihar, ma’aikatan lafiya da sauran muhimman masu ruwa da tsaki.

Ya buƙaci maniyyatan da su zama jakadu nagari ga jihar da ƙasa baki ɗaya yayin zamansu a ƙasa mai tsarki.

Labbo ya yaba wa hukumomin tsaro na jihar bisa gudanar da tantancewar maniyyata cikin sauƙi a sansaninsu da kuma a filin jirgin sama.

Haka kuma ya yaba wa Gwamnan Jihar, Malam Umar Namadi, bisa goyon baya da haɗin kai da yake bai wa hukumar a kowane lokaci.

Ya bayyana cewa jihar ta ƙarfafa maniyyatanta ta hanyar gayyatar hukumomin gwamnatin tarayya da suka haɗa da ‘Yan Sanda, Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), Hukumar Shige da Fice da kuma Kwastam, domin wayar da kan maniyyata kan abubuwan da za a iya ɗauka da kuma abubuwan da aka haramta.

Ahmed Labbo ya yi kira gare su da su ji tsoron Allah a dukkan ayyukansu yayin zamansu a ƙasa mai tsarki.

Ya ƙara da cewa jihar ta shirya komai don tabbatar da jin daɗinsu da walwalarsu a Masarautar Saudi Arabia.Wasu daga cikin maniyyatan da suka yi magana da Rediyon Najeriya kafin tafiyarsu sun yaba wa gwamnatin jihar da hukumar Hajji bisa kyakkyawar kulawa da suka samu a sansanin Hajji da kuma a filin jirgin sama.

Rahoton wakilinmu ya nuna cewa jirgin kamfanin Umza Airline ne ya ɗauki maniyyatan.

Labarai

Labarai19 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai22 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara