Connect with us

Labarai

An Gudanar Da Taron Bita Kan Dashen Koda A Kano

Published

on

Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano Farfesa Sagir Adamu, ya ce asibitin koyarwa na Aminu Kano ya gudanar da dashen koda sama da dari daya daga shekarar 2002 zuwa yanzu.

 

Farfesa Sagir ya bayyana hakan ne a yayin wani taron bitar dashen koda na yini uku da Asusun Tallafawa Manyan Makarantu na Kasa TETFUND ya shirya a asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH).

Shugaban jami’ar wanda mataimakinsa na sashen gudanarwa Farfesa Mahmud Sani  ya  wakilce shi, ya bayyana cewa, Asibitin Aminu Kano na daya daga cikin asibitocin koyarwa na Arewa da suka fara aikin dashen koda shekaru 20 da suka gabata.

Ya yabawa Asusun na TETFUND bisa kaddamar da taron shirin a AKTH tare fatan ganin dorewarsa da kuma fadada shi zuwa wasu asibitocin.

A jawabinsa Babban Daraktan Kula da Lafiya na asibitin, Farfesa Umar Gajida, ya yi nuni da cewa Asusun TETFUND ya yi ayyuka da dama a fannin dashen Koda.

 

Shugaban ’yan kwangilar da suka samar da kayan aikin dakin gwaje-gwaje Alhaji Umar Ali, ya jaddada cewa an kashe sama da Naira miliyan dari biyu don sayan kayan aikin  dashen Koda.

Wasu daga cikin mahalarta taron da suka zanta da gidan rediyon Najeriya sun yi alkawarin yin amfani da ilimin da suka samu ta hanyar da ta dace.

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa an zabo mahalarta taron ne daga asibitocin koyarwa guda shida a fadin jihohin Kano da Bauchi da Filato da Maiduguri da Abuja da kuma Kaduna, inda za a yi dashen koda har guda uku a karshen taron bitar domin likitocin su kara fahimtar aikin dashen.

Khadija Aliyu

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Ilimi1 day ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Gidaje A Jami’ar Tarayya Da Ke Babura

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta ci gaba da tallafawa harkokin koyo da koyarwa a Jami’ar Fasaha ta Gwamnatin...

Labarai2 days ago

An Samar Da Sabon Tsari Da Zai Inganta Harkar Noman Rogo A Najeriya

Shugaban kungiyar masu noman rogo ta Najeriya (NCGA), Mustapha Othman Bakano, ya kaddamar da wani tsari na samar da kasuwa...

Labarai3 days ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Tarakta 300 Ga Manoma Daga Amurka

A kokarinta na ci gaba da habbaka harkokin noma, Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙulla wata yarjejeniyar haɗin gwiwa da wasu...

Labarai3 days ago

An kama masu zanga-zanga 17 a jami’ar Texas

An sake kama ƙarin mutanen da ke da alaƙa da zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinawa inda a wannan karon...

Labarai4 days ago

An Samar Da Masauki Kusa Da Harami Ga Alhazan Jihar Jigawa

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa  ta samar da katafaren masauki  kusa da Masallacin Harami da ke birnin Makkah...

Labarai6 days ago

Kungiyar AFAN Ta Shirya Taron Bita Ga Manoman Jihar Jigawa

Hadaddiyar kungiyar manoma ta kasa reshen Jihar Jigawa da cibiyar binciken yanayin kasa dake Kaduna sun shirya wa manoma daga...

Fasaha7 days ago

An Bukaci Gwamnatin Sakkwato Ta Agaji Jami’ar Jihar

Kungiyar Malaman Jami’ar Jihar Sakkwato ASUU-SSU ta yi kira ga gwamnatin Jihar ta duba halin da kungiyar ke ciki da...

Kasuwanci7 days ago

Mun Aika Musu Takardun Gargadi Kafin Ginin Ya Rushe – KANUPDA

  Manajan Daraktan Hukumar Tsare-tsare da Ci gaban Birane ta Jihar Kano (KNUPDA), Architect Ibrahim Yakub Adamu ya yi gargadin...

Ilimi7 days ago

Zamu Zuba Jarin Dala Miliyan 600 a Nijeriya – Mr. Robert

Shugaba Kasa Bola Tinubu ya samu masu zuba jarin dala miliyan 600 daga kamfanin sufurin jiragen ruwa na kasar Denmark,...

Labarai1 week ago

Gini Ya Fado Kan Mutane 11 A Kano

Wani gini ya fado kan ma’aikata suna tsaka da aikin gini a unguwar Kuntau da ke Karamar Hukumar Gwale a...

Mafi Shahara