Labarai
Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Ta Bukaci Maniyyata Su Rika Halartar Taron Bita
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta yi kira ga maniyyatan jihar da su halarci taron bita na mako-mako da ake gudanarwa a cibiyoyin da aka kebe a fadin jihar.
Babban Daraktan Hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya yi wannan kiran a Dutse babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa kiran ya zama wajibi domin a horar da Maniyyatan rukunai da manyan ka’idojin aikin Hajji kamar yadda addinin ya koyar.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce wajibi ne kowane Maniyyaci ya samu halartar kashi 80 cikin 100 na taron bitar kafin jigilar su zuwa Saudiyya.
Ya yi nuni da cewa hukumar ta samar da matsuguni tsaftatacce ga maniyyatan jihar a kusa da Harami, inda ya kara da cewa, an kuma kara samar da tsare tsare kan yadda za a ciyar da Alhazan yayin aikin Hajjin.
Don haka ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa tallafin da yake bai wa hukumar domin gudanar da aikin Hajjin na bana.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
