Labarai
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Kayan Abinci Ga Al’ummar Najeriya
Gwamnatin Tarayya ta ce za ta fara raba hatsi a faɗin ƙasar a wani mataki na rage matsin rayuwa da ƴan Najeriya suke ciki.
Ministan aikin gona Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a yau Litinin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
“Ina bai wa ƴan Najeriya da suke cikin halin matsin rayuwa haƙuri. Na san halin ƙunci da ake ciki, musamman ganin fasa rumbunan abinci da kuma wawaso da ake yi,” in ji ministan.
Ya ce yana son ya tabbatarwa ƴan Najeriya cewa gwamnati na ci gaba da ƙoƙari na ganin abubuwa sun daidaita.
Sanata Kyari ya ce shugaban ƙasa ya amince a fara raba Hatsi da ya kai tan dubu arba’in da biyu a faɗin jihohi 36 na ƙasar a wannan mako.
“Muna aiki kafada da kafada da hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA da kuma jami’an tsaro na farin kaya DSS don tabbatar da cewa Hatsin ya kai hannun wadanda suka cancanta, wato mabukata”.
Ministan ya ƙara da cewa za a fitar da tan dubu hamsin da takwas da dari biyar na shinkafa zuwa kasuwanni a cikin farashi mai rahusa.
Har ila yau, ministan ya buƙaci ‘ƴan Najeriya da su ci gaba da mara wa gwamnatin shugaba Bola Tinubu a kokari da take yi na ganin ta shawo kan matsalolin da ƙasar ke fuskanta.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
