Labarai
Gwamnatin Tarayya ta Bada Tallafin Kayayyakin Aiki Gona ga Ƙananan Manoma a Jigawa
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin tarayya ta ce sauya fasalin bangaren noma a Najeriya ta hanyar bai wa samar da wadataccen abinci muhimmanci.
Ministan Noma da Wadata Kasa da Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana hakan yayin rabon kayayyakin noma ga kananan manoma a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.
Ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya na aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki da dama domin bunkasa samar da ayyukan yi, da kuma rage tsadar rayuwa.

A cewarsa, Ma’aikatar Noma da ta kaddamar da shirye-shirye da ayyuka da dama domin magance wasu matsalolin da manoma ke fuskanta, tare da tabbatar da wadatar abinci, samun sa cikin sauki, da kuma rage tsadarsa ga dukkan ‘yan Najeriya.
Ministan, wanda Daraktan Sashen Noman Lambu na Ma’aikatar Noma da Wadata Kasa da Abinci ta Tarayya, Alhaji Yarima Uba, ya wakilta, ya ce sun kuduri aniyar tabbatar da cewa dukkan shirye-shirye da tsare-tsaren bangaren noma na wannan gwamnati sun yi daidai da manufofin shugaban kasa.
⁹
Sanata Abubakar Kyari ya kara da cewa, gwamnatocin tarayya da na jihohi na ci gaba da hadin gwiwa domin magance dukkan matsalolin da ke shafar wadatar abinci.
A cewarsa, ma’aikatar na da kudurin karfafa hadin gwiwa da kungiyoyi da kamfanoni masu zaman kansu domin kara inganta kokarin tabbatar da wadatar abinci, bunkasar tattalin arziki, samar da ayyukan yi da rage talauci.

Ya nuna cewa, ma’aikatar ta tanadi aiwatar da tsare-tsare na gajeren lokaci da hanyoyin tallafi domin rage tsadar muhimman kayayyakin noma, tare da saukaka samunsu ga manoma ta hanyar tsari mai inganci da rikon amana.
Abubakar Kyari ya bukaci wadanda suka amfana da kayayyakin da su yi amfani da su yadda ya dace domin samar da karin abinci ga kasa.

Ya ce “Babban abin da muka sa a gaba shi ne saukaka samar da kayayyakin noma da na’urorin aikin gona masu inganci ga kananan manoma da tsadar wadannan kayayyaki ke hana su samun su, wanda hakan ke bukatar tallafi.”
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa kayayyakin da aka rabawa manoman kyauta sun hada da injinan noma da ake kerawa a nan gida Najeriya, magungunan kashe ciyawa, takin zamani na ruwa, na’u’rorin feshin magani, injinan famfon ruwa, da sauransu.
An yi rabon kayayyakin ne ta hannun kungiyoyin masu noma amfanin gona daban-daban, kungiyoyin hadin gwiwar manoma, manoma masu bukata ta musamman da kuma ‘yan gudun hijira.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
