Connect with us

Ilimi

Dalibar Jami’ar Bayero Daga Jihar Jigawa ta Sami Lambobin Yabo a Fannin Ilimin Kimiyyar Magunguna

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria 

Gwamna Umar Namadi ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na ba da kulawa, ƙarfafawa da tallafawa fitattun ‘yan asalin jihar a fannoni daban-daban na Ilimi.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake karrama wata fitacciyar ‘yar asalin Jigawa, Maryam Sulaiman Abubakar, wadda ta kammala karatun a fannin kimiyyar magunguna(Pharmacy) a Jami’ar Bayero da ke Kano, a zauren Majalisar Gwamnati da ke Fadar Gwamnati, Dutse, babban birnin jihar.

Ya bayyana cewa karfafa wadanda suka nuna hazaka na daga cikin ginshiƙan hangen nesan gwamnatinsa wajen tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.

Da yake gabatar da wadda aka karrama, Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi, Farfesa Isa Yusuf Chamo, ya bayyana cewa Maryam Sulaiman ta yi fice sosai a fannin karatunta, inda ta lashe kusan dukkanin lambobin yabo da jami’ar ta bayar a ffannin kimiyyar magunguna wato pharmacy.

A cewarsa, nasarorin da ta samu sun nuna ƙwazo, jajircewa da kuma ƙwarewa a fannin ilimi.

Ya ce Maryam Sulaiman ta samu lambar yabo ta  ƙwararryar ɗalibar da ya kammala karatun Pharm D gaba ɗaya, da lambar yabo ta kungiyar masana kimiyyar magunguna ta kasa wato Pharmacy Council of Nigeria, da  kungiyar mata masana kimiyyar magunguna wato Association of Lady Pharmacists, da kuma ta Clinical Pharmacists Association of Nigeria.

Sauran lambobin yabon sun haɗa da na Association of Hospital and Administrative Pharmacists of Nigeria, da kuma lambar yabo ta ƙwarewa daga Pharmacist Ahmed Ghana a matsayin mafi ƙwararriyar ɗalibar da ta kammala karatu daga Jihar Jigawa.

Gwamna Namadi ya taya Maryam murnar wannan gagarumar nasara ta ilimi, wadda ya bayyana a matsayin abin koyi da alfahari.

Ya gode wa Allah da ya albarkaci Jihar Jigawa da hazikan matasa kamar Maryam Sulaiman, yana mai cewa ta nuna bajinta ta musamman ta hanyar lashe manyan lambobin yabo da kuma samun kusan cikakkun maki a karatunta.

Muna alfahari da ke, kuma muna jin daɗin kasancewarki ‘yar asalin Jihar Jigawa. Nasarorinki sun sa mu alfahari.”

Namadi ya kuma nuna cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa mata domin girmama baiwar da take da ita ta musamman.

Ya ce gwamnatin jihar za ta ɗauki nauyin karatunta gaba ɗaya har zuwa matakin digirin digirgir.

Har ila yau, Namadi ya umarci Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi da ta gaggauta sauƙaƙa mata samun gurbin karatu domin ci gaba da karatunta.

Ya sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari a fannin ilimi tare da tallafawa fitattun ‘yan asalin Jigawa, a matsayin wata hanya ta gina al’umma mai ilimi, da dogaro da kai.

 

 

Labarai

Labarai18 hours ago

NEMA Da Masu Ruwa Da Tsaki Sun Kara Haɗa Gwiwa Don Hana Aukuwar Ambaliya Da Hadarin Tankar Mai

  By Adamu Yusuf   Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), tare da haɗin gwiwar masu ruwa da...

Labarai2 days ago

Kaduna Ta Kaddamarda Shirin Rabon Maganin Kariya Daga Cutar Dundumi

  Daga Khadija Kubau   Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kaduna tareda haɗin gwiwar kungiyar Sightsavers sun kaddamar da shirin raba...

Ilimi2 days ago

Hukumar Ilimantar Da Makiyaya Ta Kasa Ta Horarda Ma’aikatanta Kan Yanda Za’a Mayarda ‘Ya’yan Makiyaya Makaranta 

  By Adamu Yusuf   Hukumar Ilimantar da Makiyaya Ta Kasa (NCNE) ta shirya taron horas da ma’aikatan ta kan...

Labarai2 days ago

NCAA ta Yaba wa Hukumar Alhazai ta Jihar Kebbi Bisa Kyakkyawan Tanadin Aikin Hajji

Daga Sani Dutsinma Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya (NCAA), ta yaba da kokarin Hukumar Jin Daɗin Alhazai...

Labarai2 days ago

Sojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga 45 a Katsina

Rundunar sojin Najeriya ta kashe ’yan bindiga 45 a wani mummunan artabu da aka yi a yankin Danmusa na cikin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kebbi Ta Bukaci Malamai Su Yi Wa’azin Zaman Lafiya

Gwamnatin Jihar Kebbi ta karyata zargin cewa gwamnatin Gwamna Nasir Idris ba ta taka rawar gani wajen bunkasa harkokin addinin...

Labarai2 days ago

Ranar Mata Ta Duniya: Gwamnatin Kano Ta Bukaci A Kara Tallafa wa Mata da ’Yan Mata

Kwamishinar Harkokin Mata, Yara da Masu Bukata ta Musamman ta Jihar Kano, Amina Abdullahi, ta bukaci masu ruwa da tsaki...

Labarai2 days ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Yi Kira Da A Karfafa Mata

Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta bukaci hukumomin gwamnati, abokan hulda na ci gaba, sarakuna, malamai da...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Mutane Biyu Kan Lalata Kayan Wutar Lantarki a Nasarawa

Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da lalata igiyoyi da sandunan wutar lantarki...

Labarai2 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Biyu Da Ake Zargin ’Yan Bindiga Ne a Kwara

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya NSCDC a Jihar Kwara ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da alaka...

Mafi Shahara