Connect with us

Ilimi

Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Ba da Umarnin Rufe Makarantu 47 Nan Take

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin rufe makarantu arba’in da daya  saboda matsalolin tsaro.

A wata takardar sanarwa da aka aikewa dukkan Shugabannin makarantu, wadda Daraktan Makarantu Manyan Sakandare na Ma’aikatar Ilimi ya sanya wa hannu, gwamnati ta bayyana cewa sakamakon ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar nan da kuma buƙatar kare duk wani yunkurin hari, Ministan Ilimi ya amince a rufe makarantun nan dltaje.

Ga jerin makarantu da abin ya shafa:

  1. Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Minjibir, Jihar Kano
  2. Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Ganduje, Jihar Kano
  3. Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Zariya, Jihar Kaduna
  4. Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Kafanchan, Jihar Kaduna
  5. Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Bakori.
  6. Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Dayi, Jihar Katsina
  7. Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Daura, Jihar Katsina
  8. Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Tambuwal, Jihar Sakkwato
  9. Kwalejin Kimiyya ta Tarayya, Jihar Sakkwato
  10. Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Wurno, Jihar Sakkwato
  11. Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Gusau, Jihar Zamfara
  12. Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Anka, Jihar Zamfara
  13. Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Gwandu, Jihar Kebbi
  14. Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Birnin Yari, Jihar Kebbi
  15. Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Zuru, Jihar Kebbi
  16. Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Kazaure, Jihar Jigawa
  17. Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Kiyawa, Jihar Jigawa
  18. Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Hadejia, Jihar Jigawa
  19. Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Bida, Jihar Neja
  20. Kwalejin Gwamnatin Tarayya, New Bussa, Jihar Neja
  21. Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Kuta-Shiroro, Jihar Neja
  22. Akademiyar Gwamnatin Tarayya, Suleja, Jihar Neja
  23. Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Ilorin, Jihar Kwara
  24. Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Omu-Aran, Jihar Kwara
  25. Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Gwanara, Jihar Kwara
  26. Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Ugwolawo, Jihar Kogi
  27. Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Kabba, Jihar Kogi
  28. Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Ogugu, Jihar Kogi
  29. Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Bwari, Abuja
  30. Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Rubochi, Abuja
  31. Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Abaji, Abuja
  32. Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Potiskum, Jihar Yobe
  33. Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Buni-Yadi, Jihar Yobe
  34. Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Gashua, Jihar Yobe
  35. Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Michika, Jihar Adamawa
  36. Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Ganye, Jihar Adamawa
  37. Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Azare, Jihar Bauchi
  38. Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Misau, Jihar Bauchi
  39. Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Bajoga, Jihar Gombe
  40. Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Billiri, Jihar Gombe
  41. Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Zambuk Jihar Gombe.
  42. Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Bwari, Abuja.
  43. Kwalejin Fasaha ta Tarayya Ikare Akoko.
  44. Kwalejin Fasaha ta Tarayya Ijebu-Imusin.
  45. Kwalejin Fasaha ta Tarayya Ushi Ekiti.
  46. Kwalejin Gwamnatin Tarayya Ganye
  47. Kwalejin Gwamnatin Tarayya Billiri

Takardar ta umarci Shugabannin makarantu da abin ya shafa su tabbatar da cikakken bin wannan umarni.

 

RN

Labarai

Labarai21 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai23 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara