Connect with us

Ilimi

Gwamna Namadi Ya Tabbatar da Yunkurin Kafa Cibiyar Tarayya Ta Uku a Jigawa

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Gwamnatin Jihar Jigawa ta tabbatar da bada cikakken goyon bayanta ga Kwalejin Aikin Noma ta Gwamnatin Tarayya da ke Kirikasamma.

Gwamna Umar Namadi ya bayar da wannan tabbaci ne lokacin da ya karɓi tawagar gudanarwar kwalejin ta farko, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Dr. Muhammad Yusha’u Gwaram, yayin ziyarar girmamawa da suka kai Gidan Gwamnati da ke Dutse.

Ya taya shugaban kwalejin da tawagarsa murna, inda ya bayyana nadin nasu a matsayin tarihi kuma mai matuƙar muhimmanci.

Malam Umar Namadi ya ƙara da cewa kafa sabuwar cibiyar ilimi aiki ne babba, yana mai bayyana tabbacin cewa  mutanen da aka zaba don fara gudanar da kwalejin za su taka rawar gani.

Kafa sabuwar cibiyar ilimi ba abu ba ne mai sauƙi. Kun shiga tarihin wannan kwaleji, wacce idan ta yi nasara, za a tuna da ku cikin alheri; idan ta gaza kuma, babu shakka hakan zai shafe ku. Amma ina da tabbaci, ganin irin mutanen da ke cikin wannan tawaga, cewa kwalejin ta fara da ƙafar dama,” in ji shi.

Namadi ya bayyana godiyarsa ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da dokokin da suka kafa Kwalejin Noma ta Tarayya a Kirikasamma da Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Birnin Kudu, inda ya bayyana cewa Jigawa na kan hanyar samun wata cibiyar tarayya ta uku bayan tattaunawar da ya yi da shugaban ƙasan.

Gwamna Namadi ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da cikakken goyon baya ga tawagar gudanarwar.

 

Za mu yi duk mai yiwuwa don tabbatar da nasarar fara aiki a kwalejin, kuna da cikakken goyon bayanmu, mun yi sa’a sosai da samun Dr. Gwaram a matsayin jagoran wannan cibiyar, ƙwararren masani a fannin noma, gogaggen mai gudanarwa, kuma ɗan asalin Jigawa mai kishin ƙasa.”

Ya yaba wa Ministan Noma, Ministan Ilimi, da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Mazabar Birniwa/Guri/Kirikasamma, Alhaji Fulata, kan rawar da suka taka wajen ganin an kafa sabuwar kwalejin.

Haka kuma ya jinjinawa shugaban kwalejin da Kwamishinan Ilimi na manyan makarantu bisa jajircewarsu.

Tunda farko, shugaban kwalejin, Dr. Muhammad Yusha’u Gwaram, ya bayyana godiyarsa ga gwamnatin jihar bisa goyon bayanta, tare da jaddada cewa kwalejin ta shirya fara aiki nan take.

A cewarsa, kwalejin za ta kasance cibiya ta musamman da za a koyar da ingantattun hanyoyin noma na zamani.

Ya bayyana cewa sun shirya horas da manoma da kuma jawo hukumomin da suka dace zuwa Jihar Jigawa.

Ya ce sun fara tattaunawa da hukumomin da ke da alhakin rajista da tsari kamar NBTE da sauran da ake buƙata don fara aiki.

Ya yaba da irin  ƙoƙarin da aka yi wanda ya kai ga amincewa da kafa cibiyar, yana mai jaddada yawan tattaunawar da aka yi da hukumomin tarayya, masu tsara doka, da masu ruwa da tsaki, tare da tabbatar wa gwamna cewa tawagarsu za ta yi aiki tukuru wajen cimma nasara kwalejin.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara