Labarai
TSARO: Gwamnan Jihar Neja Ya Nuna Alhini Kan Harin ‘Yan Ta’adda a Al’ummomin Borgu
Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya bayyana matuƙar baƙin cikinsa kan harin ‘yan ta’adda da aka kai wa wasu al’ummomi a Karamar Hukumar Borgu ta jihar, wanda ya yi sanadin salwantar rayuka da dama.
A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna, Bologi Ibrahim, ya fitar wa manema labarai a Minna, gwamnan ya bayyana harin a matsayin mugun aiki da ta’asa da rashin imani, wanda ya janyo mutuwar mutane da dama, sace wasu, tare da lalata hanyoyin dogaro da rayuwar jama’a.
Gwamna Umar Bago ya miƙa ta’aziyyarsa ta musamman ga al’ummomin da abin ya shafa, musamman waɗanda harin ya rutsa da su da iyalansu a Kasuwar Daji da ƙauyen Sukumbara. Ya bayyana cewa waɗanda abin ya shafa sun haɗa da Musulmi da Kiristoci daga sassa daban-daban na Karamar Hukumar Borgu a Jihar Neja.
Gwamnan ya ce abin yana da ɗaure kai da tayar da hankali ganin an fara sabuwar shekara da irin wannan mummunan lamari. Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da dogaro ga Allah, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa na haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro domin inganta tsaro a yankunan da abin ya shafa.
A cewarsa, ƙungiyar tsaro ta haɗin gwiwa na bin sawun ‘yan ta’addan da nufin ceto waɗanda aka sace. Ya kuma yi addu’ar Allah Ya jiƙan rayukan waɗanda suka rasu, Ya kubutar da waɗanda aka sace, Ya ba waɗanda suka jikkata lafiya.
A halin da ake ciki kuma, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta bakin Mai Ba Shi Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Bayo Onanuga, ya bayar da umarni ga Sojoji, ‘Yan Sanda da DSS da su farauto ‘yan ta’addan da ke da hannu a harin Kasuwar Daji.
PR Aliyu Lawal
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
