Labarai
Karamar Hukumar Agwara ta Jinjinawa Gwamnati Bisa Tabbatar da Tsaron Rayuka da Dukiyoyin Jama’a
Daga Aliyu Lawal
Karamar Hukumar Agwara da ke Jihar Neja ta ce za ta ci gaba da hada kai da Gwamnatin Tarayya ta Jiha Neja wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’arta, musamman masu rauni.
Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Iliyasu Zakari, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya rattaba hannu da kansa, wadda ya rabawa manema labarai a Minna, babban birnin jihar Neja.
Alhaji Iliyasu Zakari, wanda ya jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyin jama’a shi ne ginshikin mulkinsa, ya kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro (NSA) Nuhu Ribadu, hukumomin tsaro da Gwamna Mohammed Umar Bago bisa rawar da suka taka wajen tabbatar da sakin dalibai ɗari da aka sace a makarantar Cocin Saint Mary’s Catholic da ke Papiri.
Alhaji Iliyasu Zakari ya ce: “Muna matuƙar godiya ga Shugaba Tinubu, Gwamna Umar Bago, Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro, Nuhu Ribadu, da jaruman jami’an tsaro bisa jajircewarsu wajen kare lafiyar ’ya’yanmu.”
Shugaban ya kuma yi kira da a ci gaba da yin addu’a da bayar da goyon baya ga hukumomi domin tabbatar da dawowar sauran ɗalibai da malamai da har yanzu ba a same su ba, yana mai cewa: “Muna da yakinin cewa, da irin wannan haɗin kai da kula da tsaro, sauran yara da malamansu za su dawo cikin iyalansu ba da jimawa ba.”
Sai dai Alhaji Iliyasu Zakari ya yi kira ga iyaye, al’ummar Neja da ’yan Najeriya gaba ɗaya da su kwantar da hankalinsu domin Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Neja na aiki tare da hukumomin tsaro wajen tabbatar da sakin sauran ɗalibai da malamai da ke tsare a hannun masu garkuwa da mutane.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
