Labarai
Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe ta Jigawa Ta Nemi Kotuna Su Daina Jan Kafa Wajen Aiwatar da Shari’a
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Jigawa ta bayyana damuwa kan jinkirin shari’a wajen gurfanar da masu laifin rashawa, inda ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 479 da suka shafi cin hanci, amana da sauran laifuka makamanta a wannan shekarar ta 2025. Shugaban Hukumar, Barista Salisu Abdul ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai kan nasarorin da hukumar ta samu da ƙalubalen da ta fuskanta a shekarar Taron manema labaran wani ɓangare ne na shirye-shiryen hukumar na bikin Ranar Yaƙi da Cin Hanci ta Duniya.
Barista Salisu Abdul ya ƙara da cewa, cin hanci babban abin da ke janyo koma-baya ne ga Najeriya a fannoni daban-daban na rayuwar jama’a da tattalin arzikin ƙasa. A cewarsa, babban burin hukumar wacce aka kafa a watan Fabrairun 2024 shi ne ƙarfafa yaƙi da cin hanci da rashawa a jihar, tare da inganta gaskiya, ɗabi’a, da amana a harkokin gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu, da al’amuran zamantakewa da tattalin arziki.
Shugaban ya ce, a wannan shekarar hukumar ta shirya horo ga manyan ma’aikatan gwamnati da jami’anta, tare da wayar da kan jama’a kan rawar da kowa ya kamata ya taka wajen yaƙi da cin hanci. “Yayin da muke ci gaba da wayar da kai sosai, za mu ƙara haɗa kai da sauran hukumomin yaƙi da cin hanci, da hukumomin gwamnati da masu zaman kansu, da jama’a domin mu fi mai da hankali wajen dakile cin hanci fiye da magance shi bayan ya faru,” in ji shi.
Ya kuma ce, hukumar za ta rungumi fasahar zamani a ayyukanta don samun ingantaccen sakamako. Barista Salisu Abdul ya bayyana cewa, daga cikin shari’o’in 479, guda 110 sun shafi cin hanci da damfarar kuɗi, yayin da 375 suka shafi rikicin kadarori, sabanin iyali, da ma’amalar kasuwanci da ta ci tura, inda aka warware shari’o’i 107 cikin sulhu.
Ya kara da cewa an dawo da fiye da Naira miliyan 385 da kadarorin da darajarsu ta kai daruruwan miliyoyi, aka kuma mika su ga masu su. Sai dai ya nuna damuwa kan yadda alkalai ke tafiyar da shari’o’in a hankali, wanda ya bayyana a matsayin babban ƙalubale da ke kawo cikas ga yaƙi da cin hanci a jihar.
Shugaban Hukumar ya kuma nemi goyon bayan kafafen yaɗa labarai a yaƙin da ake yi da cin hanci, tare da yabawa Gwamna Umar Namadi bisa goyon bayan da yake bai wa hukumar na yin aiki bisa cikakken ‘yanci ba tare da tsoma baki ba.
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
