Labarai
Allah Ya Jikan Jarman Kauru Da Ke Jihar Kaduna
Mun sami labarin rasuwar tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Kaduna, Malam Suleiman Lawal Jarman Kauru.
Malam Suleiman Lawal, mai shekaru 78, ya rasu a daren Asabar, 3 ga Janairu, 2026, bayan fama da doguwar jinya.
Kafin rasuwarsa, ya kasance Sakataren Kwamitin Aiki da cikawa (Task Force Committee) kan gina Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH), Shika, Zariya, da kuma Cibiyar kula da lafiyar Ido ta Ƙasa (National Eye Center), Kaduna.
A baya, ya riƙe muhimman mukamai da dama, ciki har da shugaban Kwalejin Fasaha ta Jihar Kaduna dake Zariya (wacce yanzu ake kira Nuhu Bamalli Polytechnic, Zariya), Kwamishinan Tarayya a Hukumar kula da da’ar Ma’aikata Federal Character Commission mai wakiltar Jihar Kaduna, da kuma Kwamishinan Ilimi na Jihar Kaduna, da sauransu.
Marigayi Jarman Kauru ya rasu ya bar mata biyu, ’ya’ya 14, da jikoki da dama.
Daga cikin ’ya’yansa akwai Alhaji Nuraddeen Suleiman Lawal Mayana Kauru, Sakataren Ilimi (Academic Secretary) na kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli, Zariya.
An gudanar da sallar jana’izan sa a Filin Eid na Mallawa da ke Ban Zazzau, Zariya, da misalin karfe 1:30 na rana, Lahadi, 4 ga Janairu, 2026.
Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa kurakuransa, Ya kuma ba shi Aljannar Firdausi.
Yusuf Zubairu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
