Labarai
Gwamnatin Kano Ta Faɗaɗa Damar Tattalin Arziki ga Mata da Masu Buƙata Ta Musamman
An kammala kasuwar baje kolin mata ta tsawon kwanaki huɗu, wadda Ma’aikatar Harkokin Mata, Yara da Masu Buƙata Ta Musamman ta Jihar Kano ta shirya, inda kowacce mahalarta ta karɓi tallafin kuɗi Naira dubu hamsin (₦50,000) domin bunƙasa da faɗaɗa kasuwancinta.
Shirin, wanda Kwamishiniyar ma’aikatar, Ambasada Amina Abdullahi Sani ta jagoranta, ya samar da dandali mai amfani ga ’yan kasuwa mata, ciki har da masu buƙata ta musamman (PWDs), domin baje kolin kayayyakinsu, sayar da su, kafa alaƙar kasuwanci da kuma samun sabbin kasuwanni.
Da take jawabi a bikin rufe taron, Kwamishiniyar—wadda Daraktar Sashen Mata, Bilkisu Shafi’u Jibrin ta wakilta—ta bayyana cewa kasuwar baje kolin na daga cikin manyan tsare-tsaren ma’aikatar na ƙarfafa tattalin arzikin mata da kuma bunƙasa ci gaba mai haɗa kowa da kowa a faɗin Jihar Kano.
Ta yaba wa mahalarta taron bisa ƙirƙira, jajircewa da ƙudurinsu na dogaro da kai a fannin tattalin arziki.
Ambasada Amina Abdullahi Sani ta jaddada aniyar ma’aikatar na ci gaba da ƙarfafa mata da masu buƙata ta musamman, tare da yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa cikakken goyon baya da jajircewarsa wajen inganta walwala da matsayin tattalin arzikin mata a Jihar Kano.
An kammala taron cikin yanayin farin ciki da godiya, yayin da mahalarta suka yi murnar cin ribar tallace-tallace, kafa sabbin haɗin gwiwar kasuwanci da kuma tallafin kuɗi da suka samu daga ma’aikatar.
Khadijah Aliyu
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
