Labarai
Babban Hafsan Sojin Sama Ya Tattauna da Tsofaffin Sojoji a Kaduna
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na inganta walwalar jami’anta, masu aiki da kuma waɗanda suka yi ritaya.
Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, ya bayar da wannan tabbaci ne a yayin taron shekara ta 2025 na tattaunawa tsakanin Babban Hafsan Sojin Sama da tsofaffin sojoji da ke zaune a Jihar Kaduna.
Air Marshal Sunday Aneke ya danganta nasarori da ci gaban da Rundunar Sojin Sama ta samu da ƙoƙari da sadaukarwar da tsofaffin sojoji suka yi a lokacin aikinsu.
Da yake wakiltar Babban Hafsan, Babban Jami’in Gudanarwa, Air Vice Marshal Anthony Martins, ya bayyana cewa domin girmama irin gudummawar da suka bayar, Rundunar Sojin Sama ta jajirce wajen kula da walwalarsu da jin daɗinsu gaba ɗaya.
A cewarsa, an tsara shirye-shiryen tallafin walwala na musamman domin tsofaffin sojoji, ba wai kawai don inganta rayuwarsu ba, har ma da ƙarfafa gwiwar jami’an da ke kan aiki, ta hanyar tabbatar musu cewa za a kula da su yadda ya kamata bayan ritaya.
Tun da farko, a jawabinsa na maraba, Kwamandan Rundunar Horar da Sojin Sama Air Vice Marshal Esen Efanga, ya bayyana cewa taron wata dama ce ta nazari kan ainihin ma’anar zama tsohon soja, tare da jaddada cewa Rundunar Sojin Sama da kuma Sojojin Ƙasa gaba ɗaya za su ci gaba da amfana da tarin gogewarsu.
A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar Walwalar Tsofaffin Sojoji, Malam Usman Yusuf mai ritaya, ya nuna matukar farin ciki, yana mai cewa taron zai taimaka matuƙa wajen inganta rayuwar tsofaffin sojoji.
Babban abin da ya dauki hankali a taron shi ne zaman tambaya da amsa kai tsaye, tare da shirye-shiryen kula da lafiya.
Usman Sani
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
