Labarai
Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Za Ta Mayar Da Rarar Kudi Ga Maniyyatan 2026
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ta shirya fara mayar da rarar kuɗin ga maniyyata, sakamakon rage kudin kujerun Hajjin 2026 da Hukumar Alhazai ta Kasa, NAHCON, ta sanar.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Habibu Yusuf Babura, ya rabawa manema labarai, ya ce Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana cewa za a mayar da rarar kuɗin ne ga maniyyatan da suka kammala biyan kudadensu a fadin jihar kafin a sanar da rage kudaden.
Ahmed Labbo ya ce NAHCON ta bayyana sabon farashin cewa yankin Arewa zai biya sama da Naira Miliyan 7.6, yayin da waɗanda za su tashi daga yankin Kudu za su biya sama da Naira Miliyan 7.9.
A cewarsa, matakin mayar da kuɗin umarni ne daga Hukumar Alhazai ta Kasa, sakamakon gagarumin ragin da aka samu.
Saboda haka, ya umarci dukkan shugabannin sassa na hukumar da su fara karɓar takardun neman mayar da kuɗi daga maniyyatan nan take.
“Muna kira ga dukkan shugabannin sassa da su gaggauta tattara takardun da ake bukata tare da bayanan asusun banki na wadanda za a mayarwa kudaden.”
Daraktan ya bukaci jami’an da su tabbatar kuɗin ya isa ga waɗanda suka cancanta ba tare da bata lokaci ba.
Ya ce shirin gudanar da aikin hajjin 2026 ya yi nisa sosai, a jihar da ma a ƙasar Saudiyya.
Ya kara da cewa hukumar na aiki tukuru don samun mafi kyawun tsari Alhazan jihar, kamar yadda aka saba gudanarwa a baya.
“Ina kuma kira ga dukkan maniyyata da su tabbatar sun biya kudadensu kafin ranar 24 ga watan Disamba don kaucewa matsaloli ko rasa damar zuwa aikin Hajjin.”
Ahmed Labbo ya yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa cikakken goyon baya da jajircewarsa ga hukumar, wanda ya ce ya kasance ginshiƙi wajen kula da jin daɗi da walwalar alhazai na jihar.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
