Ilimi
Gwamnatin Katsina Ta Umurci a Gaggauta Rufe Dukkan Makarantun Jihar
Daga Isma’il Adamu
Gwamnatin Jihar Katsina ta umarci gaggauta rufe dukkan makarantun gwamnati, da na masu zaman kansu a fadin jihar biyo bayan kalubalen tsaro da ya addabi makarantun kasar nan.
Wannan mataki na zuwa ne bayan wasu hare-haren sace ɗaliban makarantu da suka faru a jihohin Kebbi da Neja kwanan nan.
Wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare, Sani Danjuma, ya sanyawa hannu, ta ce an ɗauki wannan mataki ne domin nuna jajircewar gwamnati wajen kare ɗalibai, malamai da ma’aikatan makarantu.
Sanarwar ta ce duk da cewa rufe makarantun na iya kawo cikas ga iyaye da ɗalibai, tsaro ya fi komai muhimmanci yayin da hukumomi ke ci gaba da ƙarfafa matakan tsaro a makarantu.
Ta kuma bukaci hukumomin makarantu da su tabbatar da bin umarnin, tare da kiran iyaye da su ba da haɗin kai, a yayin da gwamnati tare da hukumomin tsaro ke ci gaba da sa ido kan al’amuran domin yiwuwar sake duba wannan mataki.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
