Labarai
Sojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga 45 a Katsina
Rundunar sojin Najeriya ta kashe ’yan bindiga 45 a wani mummunan artabu da aka yi a yankin Danmusa na cikin dajin Rugu, wurin da ’yan bindiga ke fakewa a jihohin Katsina da Zamfara.
Daga cikin wadanda aka kashe akwai fitaccen jagoran ’yan bindiga Damale, da kuma Alti, wanda yake mataimaki ga wani jagoran ’yan bindiga mai suna Adamu Alieru.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Dakta Mu’azu Danmusa, ya ce jami’an tsaro sun samu sahihan bayanai cewa ’yan bindiga na shirin kai hari kan wata al’umma da ta dakile satar shanu a yankin.
Ya ce lamarin ya fara ne a ranar 5 ga Maris lokacin da ’yan bindiga dauke da makamai suka kai hari kauyen Alhazawa a karamar hukumar Musawa domin satar shanu. Sai dai mazauna yankin tare da wasu ’yan bindiga da suka tuba suka fatattake su, inda aka kashe hudu daga cikinsu kuma aka kwato shanun.
Washegari kuma ’yan bindigar suka dawo da yawa domin daukar fansa, amma suka yi karo da sojoji na sansanin Dan-Ali, inda aka yi artabu har sojojin suka kashe dukkanin ’yan bindigar 45.
Kwamishinan ya yabawa sojoji kan kokarinsu, tare da rokon al’umma su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanan sirri domin kare yankunansu.
Isma’il Adamu/Kastina
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
