Labarai
Gwamnatin Kebbi Ta Bukaci Malamai Su Yi Wa’azin Zaman Lafiya
Gwamnatin Jihar Kebbi ta karyata zargin cewa gwamnatin Gwamna Nasir Idris ba ta taka rawar gani wajen bunkasa harkokin addinin Musulunci da ci gaban jihar ba.
Kwamishinan Harkokin Addini, Muhammad Sani Aliyu, ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a Birnin Kebbi. Ya ce zargin ba shi da tushe, kuma ya biyo bayan wata hudubar Juma’a da Bashir Jega ya yi inda ya soki gwamnati kan harkokin addini.
A cewarsa, daga cikin manyan nasarorin gwamnatin akwai kafa Ma’aikatar Harkokin Addini, wadda ya ce al’ummar jihar suka dade suna fata sama da shekaru 25 ba tare da an cimma ba.
Ya kuma ce gwamnati ta kara karfafa hukumomi kamar Hukumar Zakka da Waqafi, da Hukumar Wa’azi, da kuma Hukumar Hisbah, tare da samar musu dokoki da tallafi domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Kwamishinan ya bukaci malaman addini su mai da hankali wajen wa’azin zaman lafiya da hadin kai, tare da kauce wa shiga rigingimun siyasa da ka iya yaudarar al’umma.
Sani Haruna/Kebbi
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
