Connect with us

Labarai

Hukumar Shige da Fice ta Kasa ta Ceto Mutane 22 da Aka Yi Yunkurin Safararsu

Published

on

Daga Isma’il Adamu 

Hukumar Shige da Fice ta kasa ta ceto mutane 22 da aka yi yunkurin safararsu,  a yankin kan iyakar Zango da ke Jihar Katsina.

Kwamandan Hukumar na Rundunar Iyakokin Jibia, Haruna Zakirai ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Daura.

Ya bayyana cewa an gudanar da aikin ceton ne a sansanin sintirin jami’an hukumar da ke Daura, bayan samun bayanan sirri daga wasu mazauna yankunan da ke kan iyaka, waɗanda yi zargin wadansu  mutane yayin da suke ƙoƙarin tsallakawa da waɗanda abin ya shafa zuwa ƙetare.

Zakirai ya ce jami’ai da ma’aikatan sansanin sintiri na Daura sun gaggauta ɗaukar mataki, inda suka tare waɗanda mutanen a wani kango a ƙauyen Maibara da ke Ƙaramar Hukumar Zango ta jihar.

Ya bayyana cewa mutanen da aka ceto sun haɗa da mata 11 da maza 11, masu shekaru tsakanin 17 zuwa 35, waɗanda suka fito daga jihohi daban-daban na ƙasar nan da suka haɗa da Lagos, Osun, Rivers, Kwara, Katsina, Imo, Ondo, Benue, da Babban Birnin Tarayya Abuja.

Binciken farko ya nuna cewa ana safarar mutanen ne zuwa ƙasar Libya, daga nan kuma zuwa Turai, inda aka yaudare su da alkawarin samun ingantacciyar rayuwa.

“Wannan dabara ce da ƙungiyoyin safarar mutane ke yawan amfani da ita wajen ruɗar mutanen da ba su sani ba. Muna kira ga al’umma da su guji fadawa wannan tarko, domin a koda yaushe Hukumar Shige da Fice tana shirye wajen tarwatsa irin waɗannan ƙungiyoyi da kuma ceto mutanen da ake yunkurin safarar su,” in ji shi.

Zakirai ya ƙara da cewa akwai ɗan ƙasar Togo daga cikin mutanen da aka ceto, wanda za a mayar da shi ƙasarsa bayan kammala bincike. Ya kuma ce a yanzu haka hukumar na neman shugaban ƙungiyar masu safarar wanda aka sani da suna “Cargo” ruwa a jallo, wanda ya tsere lokacin da ake kokarin kama ‘yan ƙungiyar ta sa.

Ya jaddada ƙudirin Hukumar Shige da Fice ta kasa, na yaƙi da safarar mutane, ƙaura ba bisa ƙa’ida ba, da laifukan ketare iyaka, tare da roƙon al’umma da su rika bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai kan duk wani da ake zargi da safarar mutane.

 

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara