Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya ta Nuna Damuwa kan Jinkirin Aikin Hanyar Zariya- Sakkwato

Published

on

Ministan Ƙasa a ma’aikatar Ayyuka, Bello Muhammad Goronyo, ya bayyana damuwarsa kan jinkirin ci gaban aiki a wani sashe na aikin gina tagwayen hanyar Zariya–Funtuwa–Gusau–Talata Mafara–Sakkwato, inda ya bayyana hanyar a matsayin muhimmin aikin da ya wajaba a kammala cikin gaggawa domin ceto rayuka da bunƙasa harkokin tattalin arziki.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin ziyarar duba aikin da ake ci gaba da yi, wadda aka gudanar bisa umarnin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kuma Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi.

Da yake zantawa da manema labarai a Kilomita na 16 a kan hanyar Gusau, kusa da Bungudu, Goronyo ya ce ziyarar ta kasance ne domin tantance matakin aikin da kamfanonin da ke kula da sassa daban-daban na hanyar suka aiwatar zuwa yanzu.

Ya bayyana cewa sashen Sakkwato–Talata Mafara, wanda kamfanin CBC Construction Company ke aiwatarwa, mai tsawon kimanin kilomita 105, ya kai kusan kashi 27 cikin 100 na kammala aiki, inda ya yaba da ingancin aikin da ake yi a yankin.

A cewarsa, an taɓa tsallake wasu sassan hanyar ne a baya sakamakon rashin biyan diyya ga al’ummomin da aikin ya shafa, matsalar da ya ce an riga an warware ta.

Bello Goronyo ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu Sokoto, ya biya sauran diyya da ake bi, inda ya yaba masa ƙwarai bisa goyon bayan da yake bai wa Gwamnatin Tarayya da Shugaban Ƙasa.

Ya ce an umarci kamfanin CBC da ya koma waɗancan sassan da aka tsallake domin kammala su, don tabbatar da cikakkiyar hanya mai laushi ba tare da wata matsala ba.

Sai dai Ministan ya nuna rashin jin daɗi kan yadda aikin ke tafiya a sashen da kamfanin Triacta Nigeria Limited ke gudanarwa, inda ya ce kamfanin ya kai kashi 16 cikin 100 kacal na aiki duk da cewa an ba shi kwangilar a kusan lokaci guda tun Mayun 2023.

“Wannan hanya na da matuƙar muhimmanci. ‘Yan Najeriya na shan wahala. Hatsarori na yawaita, kuma tafiyar daga Sakkwato zuwa Gusau, wadda ya kamata ta ɗauki awa ɗaya da rabi, yanzu tana ɗaukar awanni huɗu zuwa biyar. Wannan ba abin yarda ba ne,” in ji Goronyo.

Ministan ya bayyana cewa lokacin kammala aikin gaba ɗaya an sa shi ne a shekarar 2028, inda ya sake jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na gina hanyoyi masu ɗorewa ta amfani da fasahar kankare mai ƙarfe, yana mai danganta lalacewar hanyoyin kwalta da yawan lodin manyan motoci.

A ziyarar, Ministan ya samu rakiyar wasu Daraktoci na Ma’aikatar Ayyuka, da kuma Kontarola na Ma’aikatar Ayyuka a Jihar Zamfara.

AMINU DALHATU

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara