Labarai
Rundunar ‘Yan Sanda ta Kebbi Ta Kama Dan Damfara
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kebbi ta kama wani mutum mai suna Hamza Abdullahi Sama, mazaunin unguwar KCC a Birnin Kebbi, bisa zargin damfarar sama da mutum 175 da ke neman aikin yi, a ƙarƙashin hujjar samar musu da ayyukan shirin ciyar da ɗalibai a makarantu da gwamnatin jiha ta amince da su.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Bashir Usman, ne ya sanar da hakan yayin da yake yi wa manema labarai bayani a Birnin Kebbi, babban birnin jihar.
SP Bashir ya ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin ya yi karya ta hanyar bayyana kansa a matsayin wanda Gwamnatin Jihar Kebbi ta bashi damar shirya daukar ma’aikata a makarantun firamare da sakandare.
Ya ce bisa wannan ƙaryar wakilci, waɗanda abin ya shafa—ciki har da Shafa’atu, Yusuf Yahaya, Hussaini Sani, Ubaida Abubakar, da sauransu sun yarda suka biya Naira dubu talatin kowanne, a matsayin kudaden kafin alkalami na wasu abubuwa kafin basu aikin.
SP Bashir ya ƙara da cewa ƙarin bincike ya tabbatar da cewa wanda ake zargin ya damfari jimillar Naira miliyan 5 da dubu 200 daga hannun waɗanda abin ya shafa, ta hanyar yaudara da gangan, domin babu irin waɗannan guraben aiki, kuma ba a ba shi izini daga kowace hukuma ta gwamnati ba don ɗaukar ma’aikata ko sarrafa ayyuka a madadinta.
A halin yanzu, wanda ake zargin na tsare a hannun ‘yan sanda, kuma bincike na ci gaba da gudana da nufin gurfanar da shi gaban kotu bayan kammala bincike. Rundunar ta kuma ja hankalin al’umma da su kasance masu faɗake da taka-tsantsan daga mutanen da ke cin moriyar halin ƙunci na masu neman aiki ta hanyar shirya aikin yi na bogi.
SANI DUTSINMA
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
