Ilimi
An Aika Dan Canji Da Dan Walawala Gidan Yari A Kwara

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Ilorin, karkashin jagorancin Mai shari’a Abimbola Awogboro ta yanke wa Musa Buba hukuncin daurin sa’o’i 300 da hidimar al’umma, bisa samunsa da laifin gudanar da harkokin kasuwanci na canji ba tare da wani cikakken lasisi ba.
Hakazalika, alkalin ya kuma yanke hukuncin daure wani Akinwale Olamilekan daga Owena Ijesha a karamar hukumar Oriade ta jihar Osun, daurin sa’o’i 300 (dari uku) da yiwa al’ummar hidima na tsawon sa’o’i biyar a kowace rana ba tare da zabin biyan tara ba, bayan da ya same shi da laifin aikata laifukan da suka shafi yanar gizo wato walawala ko yahoo boyi.
Hukumar dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta gurfanar da Musa da Akinwale a gaban kotu a ranar Alhamis, 20 ga Maris, 2025.
Ana tuhumar Musa Buba a wani lokaci a watan Yulin 2024 a kasuwar Chikanda, gundumar Yashikira, a karamar hukumar Baruten, jihar Kwara, yana gudanar da harkokin wata cibiyar hada-hadar kudi, Bureau De Change Business, ba tare da wani sahihin lasisi da babban bankin Najeriya ya bayar ba.
Laifin ya ci karo da Sashe na 57 (1) & (2) na Dokar Bankunan da Sauran Cibiyoyin Kudi, 2020, kuma ana hukunta shi a karkashin sashe na 57(5) (b) na wannan dokar.”
A cikin tuhumar da ake wa Akinwale Olamilekan (Alias: Mary Williams), an zarge shi da samun wani lokaci a watan Nuwamba 2024, da damfara da wata Mary Williams ta hanyar sakon karta kwana na iMessage asusu don karbar kudi $950 (Dalar Amurka Dari Tara da 55) daga wani Mark Durham.
Laifin ya sabawa sashe na 22 (2) (b) (ii) na laifukan Intanet (Hana, Rigakafin, da sauransu) Doka kuma ana hukunta shi a ƙarƙashin sashe na 22 (2) (b) (iv) na wannan Dokar.
Wadanda ake tuhumar sun amsa laifinsu.
Da yake tabbatar da gaskiyar lamarin, hujjojin da masu gabatar da kara karkashin jagorancin Andrew Akoja suka gabatar da kuma kararrakin wadanda ake tuhumar, mai shari’a Awogboro ya yanke musu hukunci daidai laifin da suka aikata.
Baya ga hukuncin, kotun ta umurci Musa Buba da ya bata kudaden da suka kai CFA 409,500 da kuma Naira 1,973,200 (Miliyan Daya, Dari Tara da Dubu Saba’in da Uku, Naira Dari Biyu Kadai) ga gwamnatin tarayya.
Hakazalika, Alkalin ya umarci Akinwale da ya ba Gwamnatin Tarayya dalar Amurka $450 (Dalar Amurka dari hudu da hamsin), da kuma wata wayar iphone 12 Pro Max da ya yi amfani da ita wajen aikata laifin.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
-
Labarai4 days ago
Al’ummar Babura Sun Karrama Sabon Shugaban Asibitin Koyarwa Na Rasheed Shekoni
-
Labarai6 days ago
Gwamna Namadi Ya Bada Aikin hanyoyi 47 masu nisan kilomita 800 a sassan jihar.
-
Ilimi5 days ago
Tsangayar Ilimi Ta BUK Ta Yi Bikin Cika Shekaru 50 Da Kafuwa
-
Ilimi3 days ago
An Fara Bada Horo Ga Masu Horas da Maniyatan Bana A Jigawa
-
Kasuwanci2 days ago
Hukumar NSCDC ta tura jami’an tsaro 415 domin aikin Easter a Zamfara.
-
Labarai4 days ago
KADGIS Za Ta Yi Amfani Da Sabuwar Manhajar Biyan Diyyar Filaye A Kaduna
-
Labarai7 days ago
Hajjin 2025: Shirye-shirye Sun Yi Nisa A Jihar Jigawa
-
Labarai3 days ago
Hukumar Alhazai ta Jigawa Ta Shirya Bitar Ga Malaman Bita na Kananan Hukumomi 27