Labarai
CORET Ta Raba Takardun Rijista Ga Shugabannin Kungiyoyin Haɗin Kai A Kaduna

Kungiyar Haɗin Kan Masu Kiwon Gargajiya ta Afirka (CORET) ta raba takardun rijista guda goma sha uku ga shugabannin kungiyoyin haɗin kai akan kiwon shanu a Ladduga, karamar hukumar Kachia ta Jihar Kaduna.
Mai kula da ayyukan CORET, Dr. Umar Hardo ne ya mika takardun a ƙarshen wani taron horaswa na kwanaki biyu da aka shirya domin wasu daga cikin shugabanni da matasan kungiyoyin haɗin gwiwa a yankin.
Taron horaswar, wanda ya ɗauki kwanaki biyu, CORET ta shirya shi tare da haɗin gwiwar ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) da kuma tallafin hukumar ci gaban Swiss Development Cooperation, ya samu goyon bayan wasu ƙungiyoyi da suka haɗa da Hukumar Koyar da Makiyaya ta Ƙasa, da Milk Value Chain Foundation da sauransu.
Dr. Umar Hardo, yace suna sa ran su ga cigaba a tsakanin dukkanin kungiyoyin hadin kai da suka samu horon musamman na samarda isasshen madara da kuma fitarda shi fiye da da.
Yace HORET tana sa ran ta ga karin samun madara da za’a rinka fitarwa daga yankin Ladugga da kuma Mai-Gatari a jihohin Kaduna da Jigawa.
Dr. Umar Hardo ya ce suna sa ran za’a rinka fitar da madara fiye da da, kuma tsatatace da zai kawowa wadannan kungiyoyin kuden shiga.
Wadda ya gabatar da kasida kuma tsohon Daraktan Ci gaban Al’umma da Kungiyoyin Haɗin Kai a Jihar Kaduna, Mista Yohanna Kabirat, yace ana sa ran mahalarta taron su iya tafiyar da Kungiyoyisu ba tareda wata matsala ba domin inganta harkar kiwon shanu da samar da madara.
Shi ma da yake jawabi, Shugaban Kungiyar Haɗin Gwiwar Ladduga, Salihu Yunusa, ya tabbatar da cikakken goyon bayan kungiyar ga matasa domin cimma burinsu.
Wasu daga cikin mahalarta sun bayyana jin daɗinsu kan horon, inda suka bayyana abubuwan da suka koya da kuma irin ƙwarewar da suka samu a lokacin taron.
Lawal Boro daga Hukumar Koyar da Makiyaya ta Ƙasa ne ya rufe taron da wata waka ta Fulatanci mai cike da ƙayatarwa da ƙarfafa gwiwa, wanda ya sa mahalarta taron suka fita da shauƙi da kwarin gwiwa.
COV: Adamu Yusuf
-
Labarai4 days ago
Al’ummar Babura Sun Karrama Sabon Shugaban Asibitin Koyarwa Na Rasheed Shekoni
-
Labarai6 days ago
Gwamna Namadi Ya Bada Aikin hanyoyi 47 masu nisan kilomita 800 a sassan jihar.
-
Ilimi5 days ago
Tsangayar Ilimi Ta BUK Ta Yi Bikin Cika Shekaru 50 Da Kafuwa
-
Ilimi3 days ago
An Fara Bada Horo Ga Masu Horas da Maniyatan Bana A Jigawa
-
Kasuwanci2 days ago
Hukumar NSCDC ta tura jami’an tsaro 415 domin aikin Easter a Zamfara.
-
Labarai4 days ago
KADGIS Za Ta Yi Amfani Da Sabuwar Manhajar Biyan Diyyar Filaye A Kaduna
-
Labarai7 days ago
Hajjin 2025: Shirye-shirye Sun Yi Nisa A Jihar Jigawa
-
Labarai3 days ago
Hukumar Alhazai ta Jigawa Ta Shirya Bitar Ga Malaman Bita na Kananan Hukumomi 27