Connect with us

Labarai

Masarautar Saminaka ta Bukaci Hadin Kai Don Dorewar Zaman Lafiya a Yankin

Published

on

Daga Yusuf Zubairu

Majalisar Masarautar Saminaka da ke Jihar Kaduna ta yi kira ga al’ummomin da ke Karamar Hukumar Lere da su rungumi hadin kai da fahimtar juna domin samar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.

Sarkin Saminaka, Alhaji Musa Sani Ibrahim, ya yi wannan kira a fadarsa yayin ziyarar gaisuwar Sallah da masu rike da sarautun gargajiya suka kai masa a lokacin bikin Eid al-Fitr.

Sarkin ya bukaci mazauna yankin da su ci gaba da rayuwa cikin zaman lafiya da jituwa ba tare da la’akari da bambancin kabila ko addini ba, yana mai jaddada cewa hadin kai shi ne ginshikin ci gaba.

Har ila yau, ya yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su kara kaimi wajen samar da kayan aikin noma da kuma magance matsalar tsaro, domin bai wa manoma damar gudanar da ayyukansu cikin sauki, wanda hakan zai taimaka wajen tabbatar da wadatar abinci.

Yayin da yake gode wa masu rike da sarautun gargajiya bisa goyon baya da biyayya da suke nuna wa masarautar, Sarkin ya bukace su da su ci gaba da zama jakadu nagari tare da mara wa gwamnati mai ci baya domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba.

A nasa jawabin, Egwe na al’ummar Igbo a Saminaka, Mista John Eze, ya nuna godiya ga majalisar masarautar bisa shugabanci mai hada kai da adalci.

Mista Eze ya yabawa salon jagorancin Sarkin, tare da jaddada kudirin al’ummar Igbo na bada gudunmawarsu wajen ci gaban yankin.

Shi ma da yake jawabi, Tafarkin Saminaka, Alhaji Musa Suleiman Tanko, ya bayyana masarautar a matsayin daya daga cikin mafi zaman lafiya a Jihar Kaduna, tare da tabbatar da cewa sarakunan gargajiya za su ci gaba da aiki tukuru domin dorewar zaman lafiyar da ake da shi domin amfanin kowa.

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara