Ilimi
Dr. Builder Muhammad Uba Ya Jagoranci Rangadin Makarantu a Birnin Kudu
Daga Usman Muhammad Zaria
Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa, Dakta Builder Muhammad Uba ya bayyana ilimi a matsayin ginshiƙin ci gaban kasa.
Ya bayyana hakan ne lokacin da ya jagoranci wata tawaga domin zagayawa makarantun yankin, don duba yadda ake koyarwa da kuma hanyoyin ilmantarwa.

A cewarsa, ziyarar na daga cikin ƙoƙarinsa na inganta tsarin ilimi a ƙaramar hukumar Birnin Kudu, wanda ya yi daidai da kudurori 12 na Gwamna Umar Namadi.
Muhammad Uba ya kuma duba wasu makarantu daban-daban, inda ya tattauna da malamai da ɗalibai domin tantance ci gaba da kuma gano wuraren da ke buƙatar gyara.

Wannan ziyara ta biyo bayan wasu sabbin ci gaba a ɓangaren ilimi na ƙaramar hukumar, ciki har da bayar da sabuwar mota ga Hukumar Ilimi ta Ƙaramar Hukuma daga Gwamnatin Jihar Jigawa ta hannun Ma’aikatar Ilimin Firamare.
Shugaban ƙaramar hukumar ya kuma tabbatar da an saka sabbin tayoyi a motar, wanda ke nuna jajircewarsa wajen tallafa wa ilimi a yankin.

A nasa jawabin, shugaban hukumar Ilimin Bai Daya na jihar (SUBEB), Haruna Idris Hadejia, ya yaba wa shugaban ƙaramar hukumar bisa ƙoƙarinsa da jajircewarsa wajen bunƙasa ilimi a Birnin Kudu.
Ya bayyana Dakta Builder Muhammad a matsayin jajirtacce da ya yi fice a Jihar Jigawa, inda ya nuna yadda yake da himma wajen aiwatar da ayyukan ci gaban ilimi.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
