Connect with us

Labarai

Hajjin 2026: Jigawa ta Kammala Samun Biza ga Dukkan Maniyyatan Jihar

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta fara raba kayan sawa (uniform) da kayan tafiya ga maniyyatan hajjin shekarar 2026.

Shugaban Hukumar kumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan ga wakilin Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar.

Ya bayyana cewa ƙaddamar da wannan shiri na rabon kayan wani ɓangare ne na shirye-shiryen gudanar da aikin hajjin bana. Yana mai cewa tuni hukumar ta fara bai wa jami’an yankuna da cibiyoyi kayan sawa da jakunkuna domin su rarraba wa maniyyata.

Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce, ya zuwa yanzu hukumar ta samu nasarar kammala dukkan biza na maniyyatan jihar, tare da kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin sauƙaƙa jigilar maniyyatan cikin kwanciyar hankali.

Daraktan ya ce Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON ta tsara fara jigilar rukuni na farko na maniyyatan Jigawa daga Filin Jirgin Sama na Nuhu Muhammadu Sunusi da ke Dutse zuwa ƙasar Saudiyya a ranar 4 ko 5 ga watan Mayu, 2026.

Ahmed Labbo ya kuma bayyana cewa Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta bai wa kamfanin jiragen sama na Umza Air alhakin jigilar maniyyatan Jigawa zuwa Saudiyya.

A cewarsa, nan ba da jimawa ba za a fara yi wa maniyyata allurar rigakafi a hedikwatar hukumar da sauran cibiyoyin da aka tanada a fadin jihar.

Shugaban hukumar ya buƙaci maniyyata su kasance masu halartar darussan horaswa a ae yi a kullum, tare da zama jakadu nagari ga jihar da ƙasa baki ɗaya.

Ya kara da cewa jami’an hukumar, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki za su fara zagayen cibiyoyin horaswa domin wayar da kan maniyyata kan matakan tsaro, lafiya da tsafta yayin zaman su a sansani da kuma a ƙasa mai tsarki.

A ƙarshe, ya yaba wa Gwamna Umar Namadi da dukkan masu ruwa da tsaki bisa goyon baya da haɗin kai da suke bai wa hukumar domin gudanar da aiki cikin nasara ba tare da wata tangarda ba.

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara